Gwamnatin Adamawa ta bude wuraren koyon karatu a kananan hukumomi shida
Ma’aikatar Ilmantar da jama’a ta bude wuraren koyon karatu a garuruwa 21 wadanda suke karkashin kananan hukumai shida. Daraktar ma’aikatar ilmantar da jama’a ta Jahar Adamawa, Madam Charity Dubi ce ta bayyana hakan. Dubi ta ce bangarorin da suka mori wannan aiki sun kunshi kananan hukuman Demsa da Gombi da Numan da Michika da Yola […]

Ma’aikatar Ilmantar da jama’a ta bude wuraren koyon karatu a garuruwa 21 wadanda suke karkashin kananan hukumai shida. Daraktar ma’aikatar ilmantar da jama’a ta Jahar Adamawa, Madam Charity Dubi ce ta bayyana hakan.
Dubi ta ce bangarorin da suka mori wannan aiki sun kunshi kananan hukuman Demsa da Gombi da Numan da Michika da Yola ta Arewa da kuma Yola ta Kudu, inda ta ce gwamnatin tarayya ta sanya malamai 21 a wadannan wurare domin taimakawa jama’a. Ta kuma kara da cewa wannan cigaban da aka samu na da alaka da irin himmar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi domin ilmantar da jama’a ta hanyar yaki da jahilci.
Ta ce gwamnatin jiha kuma ta bada nata goyon bayan, akan aikata hakan ta hanyar bayar da takardu da biro da dai makamantansu wajen taimakawa da yaki da jahilci.
Tana mai cewa a halin yanzu suna da dalibai tsoffi da manya dubu daya da dari biyu da tamanin da tara wadda suka kunshi mata 1,008 da maza 281 a jahar.