Gwamnatin Afghanistan ba za ta amince da Amurka ba – Shugaba Karzai

Shugaba Hamid Karzai na kasar Afghanistan, ya bayyana wa mahukunta a birnin New Delhi ta kasar Indiya cewa kasarsa ba za ta “amince” da Amurka ba, inda ya zargi Amurkawa da aikata sabanin abin da suke fada a kasarsa da rikici ya baibaye.Shugaba Karzai ya tabbatar wa manema labarai cewa babu abin da zai “razana […]

Gwamnatin Afghanistan ba za ta amince da Amurka ba – Shugaba Karzai

Shugaba Hamid Karzai na kasar Afghanistan, ya bayyana wa mahukunta a birnin New Delhi ta kasar Indiya cewa kasarsa ba za ta “amince” da Amurka ba, inda ya zargi Amurkawa da aikata sabanin abin da suke fada a kasarsa da rikici ya baibaye.
Shugaba Karzai ya tabbatar wa manema labarai cewa babu abin da zai “razana shi” har ta kai ga ya sanya hannu a kan yarjejeniyar tsaro, da za ta bai wa sojojin Amurka damar ci gaba da zama a kasarsa a karshen shekara mai zuwa.
“Ban amince da su ba,” inji Karzai, kamar yadda ya bayyana a wata tataunawa da ya yi da manema labarai a wani karamin otal, inda ya fito da wata wasika da Shugaba Barack Obama ya aike masa, wadda ta tabbatar da cewa rundunar sojan Amurka za ta kula da “mutuntakar” tsaron al’ummar Afghanistan a kasarsu ta haihuwa.
Gwamnatin Amurka ta tattara kwarin gwiwarta a kan cewa mahukuntan Indiya za su shawo kan Shugaba Karzai ya sanya hannun kan yarjejeniyar tsaro da suke shirin kullawa da kasarsa. Karzai, wanda a da ya amince da yarjejeniyar tsaro ta hadin gwiwa, wato “BSA,” a halin yanzu ya bijire mata.
Tunda ana sa ran zai sauka daga mukaminsa, bayan an gudanar da zaben kasa, a watan Afrilu mai zuwa, ya ce sai dai in ya sauka daga mulki a shekara mai zuwa a sanya hannu kan yarjejeniyar. Wannan matsaya da Shugaba Karzai ya tsayu a kanta, ta harzuka jami’an hukuma da ’yan majalisar Amurka, wadanda suka yi barazanar ficewa da daukacin sojojinsu matukar ya ki sanya hannu nan da karshen wannan shekarar .
“Lokacin da Obama ya rubuto mini wasika cewa zai kula da hakkkin mutanenmu na gida, na bukaci ya aiwatar da abin da ya rubuta a wasikar,” inji Karzai.
“Ka yi umarnin a daina ruwan bama-bamai, sannan a kaddamar da shirin zaman lafiya a bainar jama’a,” inji shi.
kasar Indiya dai ta yi alwashin yin duk abin da ya dace don gain al’amuran sun daidaita a Afghanistan. Shugaba Karzai dai ya gana da Firayiminista Manmohan Singh da Ministan Harkokin Waje, Kapil Sibal.