Gwamnatin APC ba ta tsinana komai ba, Inji Rimin Zayam
Jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Bashir Bukar Rimin Zayam ya ce gwamnatocin da jam’iyyar APC take jagoranta a matakin tarayya da jihohi ba su tsinana komai ba. Ya yi furucin ne a Bauchi a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan batutuwa da dama da suka shafi kasar […]

Jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Bashir Bukar Rimin Zayam ya ce gwamnatocin da jam’iyyar APC take jagoranta a matakin tarayya da jihohi ba su tsinana komai ba.
Ya yi furucin ne a Bauchi a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake yi wa manema labarai bayani kan batutuwa da dama da suka shafi kasar da kuma kalubalen da kasar ke fuskanta tun lokacin da gwamnatin Shugaba Buhari ta karbi ragamar mulkin kasar nan.
“Rudani, kiyayya da rikice-rikice ya dabaibaye jam’iyyar APC amma za su iya maganinsu idan suka kwaikwayi salon mulkin shugabannin jamhuriya ta farko da ta biyu. Dole su saurari mabiyansu, su gano matsalolinsu tare da maganinsu da kuma bunkasa su. Ya zama wajibi shugabannin jam’iyyar APC su rika girmama duk wadanda suka bayar da gudunmawar samun nasarar gwamnati su matso da su kusa. Ta haka ne za su ci gaba tare da fahimtar matsalolinsu kuma ta haka ne za su rika jin suka mai ma’ana da za ta taimaka musu samun nasarar mulkin kasar”. Inji shi.