Gwamnatin APC ta gaza a Yobe – Maina Waziri
dan takarar Gwamnan Jihar Yobe a karkashin Jam’iyyar PDP Alhaji Adamu Maina Waziri ya zargi gwamnatin jihar a karkashin Jam’iyyar APC da gaza tabuka abin kirki wajen aiwatar da muhimman ayyuka ga al’ummar jihar musamman a fannin ciyar da ilimi kiwon lafiya da samar da ruwan sha mai inganci gaba. Alhaji Adamu Waziri wadnda wannan […]
dan takarar Gwamnan Jihar Yobe a karkashin Jam’iyyar PDP Alhaji Adamu Maina Waziri ya zargi gwamnatin jihar a karkashin Jam’iyyar APC da gaza tabuka abin kirki wajen aiwatar da muhimman ayyuka ga al’ummar jihar musamman a fannin ciyar da ilimi kiwon lafiya da samar da ruwan sha mai inganci gaba.
Alhaji Adamu Waziri wadnda wannan ne karo na hudu da yake tsayawa takarar Gwamnan Jihar ya bayyana haka ne a wajen gangamin yakin neman zabensa da aka gudanar a filin wasa na 27 Augusta da ke Damaturu.
Alhaji Adamu Maina ya ce tun daga 1999 shugabannin jihar a karkashin jam’iyyun APP da ANPP da sabuwar Jam’iyyar APC suke mulki amma har zuwa yau jihar ita ce ke baya a tsakanin jihohin kasar nan 36 wajen ci gaban ilimi wanda shi ne ginshikin kowace al’umma.
Alhaji Maina Waziri ya ce, baya ga koma baya ta fuskar ilimi har ila yau ta fuskar samar da ruwan sha ma jihar na baya domin mafi yawan yankunan karkarar jihar na samun ruwa a gulabe da rafukan da dabbobi ke shan ruwa ciki, wanda hakan na kawo barazana ga lafiya.
dan takarar ya kalubalanci al’ummar jihar su farka daga barci don gano irin illar da shugabannin jihar ke yi musu ta wajen kasa sauke nauyin da ke kansu.
Ya yi zargin cewa, rashin kula da tsaron rayukansu da dukiyoyin al’ummar jihar sakaci ne na gwamnatin jihar domin rikicin ’yan kungiyar Boko Haram sakacin gwamnatin jihar ke kan gaba wajen kara rura wutarsa.
Daga nan sai ya karbi wasu jiga-jigan Jam’iyyar APC da suka canja sheka zuwa PDP da suka hada da tsohon shugaban Jam’iyyar ANPP a jihar Alhaji Sani Inuwa Nguru da tsofaffin kwamishinoni da suka hada da Alhaji Sani Chiromari da Hajiya Fatsuma Tolba da Alhaji Habu Dauda Gulani da Alhaji Jamilu Ahmad da wasu tsofaffin shugabannin kananan hukumomin Fune da Jakusko da wasu ’yan majalisar dokokin jihar masu ci daga kananan hukumomin Damaturu da Gujba.
Gangamin ya samu halattar ’ya’yan Jam’iyya PDP daga sassan jihar ciki har da tsohon Minista a Ma’aikatar Kudi Alhaji Yerima Lawan Ngama da kuma Minista a Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha Alhaji Abdul Bulama da shugaban riko na jam’iyyar Alhaji Sule Doguwa da shugaban matasan jam’iyyar Alhaji Adamu Bomboy da sauransu.