Gwamnatin APC ta tunkari dimbin matsaloli a kwana dubu

‘Wasu na yabo wasu na suka.’ A kwana a tashi ranar 22/ 02/2018, ita ce a nau’in lisssafin ta zamo cikar Gwamnatin APC kwanaki dubu cur, wanda hakan ke nuni da makonni 142 da kwanaki shidda da watanni 32, da kwanukka 11, duka dai ni har yanzu ina kyautata wa wannan gwamnatin tsammani, domin ai […]

Gwamnatin APC ta tunkari dimbin matsaloli a kwana dubu

‘Wasu na yabo wasu na suka.’ A kwana a tashi ranar 22/ 02/2018, ita ce a nau’in lisssafin ta zamo cikar Gwamnatin APC kwanaki dubu cur, wanda hakan ke nuni da makonni 142 da kwanaki shidda da watanni 32, da kwanukka 11, duka dai ni har yanzu ina kyautata wa wannan gwamnatin tsammani, domin ai game kowa da komai sai Allah, kuma a kan auna rinjayen mutum, inda ya fi a nan ne ake yimasa hukunci, imma ta nasara ko akasin ta. da fatan duk wani ko wata a cikin al’ummomin Najeriya mu nutsu, musamman talakkawa, mu gane cewa wannan gwamnatin ta zo ta tarar da manyan matsaloli, kuma gyara har abada ya fi barna sauki ku shaida ne a sanin hakan, misalai na kur kusa su ne ni da ku kowa ya waiga a ina ne yake da matsala a rayuwa ya gyara, a ina ne ake da abin kwarai a dora hakan ake bukata ba bibiyar laifin shugabanni ba.

Ai shi laifi tudu ne, kuma mu kalli kadan daga matsalolin da Baba Buhari ya tarar, inda ya gaji matsalar Boko Haram, wacce bayan kashe dubban jama’a hatta garkuwa da mutane duk ta yi kafin zuwan Buhari, wanda ’yan matan makarantar garin Chibok suna a mugun hannu na boko haram, amma sai ga kaso mai yawa a kwanaki dubu an kubuto da su, 

Haka a wannan makon ne wasu da ake jin cewa ’yan Boko Haram ne suka je a wata makaranta ta Jihar Yobe, inda suka yi gaba da ’yan mata, amma kwanaki kadan ana kokarin kubuto da su, 

Sannan matsalar ta masu fasa bututan mai da ta yi kamaria yankunan Neja Delta, inda a yau waccan barazana ta yi sauki. Kuma ga ’yan a ware na masu fafutikar Biyafra na kabilar Inyamurai, wato su Namdi Kalu, wanda yau ko motsinsa ba a ji a wannan kasa mai fadin gaske.

Masu garkuwa da mutane su ma ana kama su, har ma wadanda bas u shiga hannun hukuma ba na kashe wasu a wajen artabu. Amma kawai sai ce-ce-ku-ce na shaci fadi, wanda da dama rashin godiya ne. Domin idan an ce yunwa ake yi, shin a ina aka ce ga yunwa ta hallaka wasu mutane kimanin goma ko biyar, amma ni da ku mun tabbatar cewa ’yan ta’adda na boko haram sun sha hallaka mutane sama da 50 a lokaci guda, misalain hakan a shekara ta 2014 a babban masallaci na Jihar Kano, da hatta a wata hedkwata ta ’yan sanda; kai a majami’u an sha samun kai hare-hare na ’yan boko haram baya ga kasuwanni.

Haka lamarin  ’yan satar mutane da ke garkuwa da su duka ba su bambance waccan Bahaushe ne ko Inyamuri ko Bayarabe ko kuwa Musulmi ne ko Kirista, ko ma wane ne shi dan ta’adda bai da kama, amma kawai wasu ’yan uwana talakkawa butulci yasa sun mayar da hankulla a kan far’fagandar yunwa bayan kuwa duk da cewa ita yunwa musiba ce ai zaman lafiya ya fi a samu abinci ba nutsuwa.

Da fatan Gwanmnatin APC ta tarayya da wacce ke shugabanci a jiharmu Katsina da duk inda wasu ’yan majalisa suke a jiha ko a matakin tarayya, kai hatta daraktoci da kwamishinoni masu nagarta duka Allah ya yi musu jagora. A shrye muke mu ba su kuri’u na tazarce a zaben 2019 In sha Allah.

Mukhtar Ibrahim Saulawa, ya rubuto makalarsa daga Katsina 07066434519/08080140820