Gwamnatin Bauchi za ta inganta kafafen watsa labarai don tafiya da zamani

Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya bayyana niyyarsa ta taimaka wa kafafen watsa labarai a Jihar Bauchi don su tafi daidai da zamani.Gwamnan ya bayyana haka ne a wurin bikin bude Cibiyar ’Yan jarida ta Jihar wadda gwamnatinsa ta yi wa kwaskwarima kan milyoyin Naira, a shekaranjiya Laraba.Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta yi wannan […]

Gwamnatin Bauchi za ta inganta kafafen watsa labarai don tafiya da zamani
Gwamnatin Bauchi za ta inganta kafafen watsa labarai don tafiya da zamani

Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda ya bayyana niyyarsa ta taimaka wa kafafen watsa labarai a Jihar Bauchi don su tafi daidai da zamani.
Gwamnan ya bayyana haka ne a wurin bikin bude Cibiyar ’Yan jarida ta Jihar wadda gwamnatinsa ta yi wa kwaskwarima kan milyoyin Naira, a shekaranjiya Laraba.
Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta yi wannan aiki ne don inganta aikin jarida kamar yadda ake yi a kasashen da suka ci gaba domin kusantar da jama’a ga gwamnati. Ya ce kafafen watsa labarai mallakar jihar an mayar da su na zamani inda aka inganta gidan rediyo da talabijin da sababbin na’urori aka kuma gina sababbin gidajen rediyon al’umma a kananan hukumomi 20 na jihar.
Shugaban kungiyar ’Yan jarida ta kasa (NUJ) Malam Mohammed Garba ya gode wa gwamnatin Jihar Bauchi game da gyaran da ta yi ga cibiyar wadda ya ce ba kamarta a kasar nan.
Ya shawarci ’yan jarida su rika kare martabar aikin ta hanyar nuna kwarewa lokacin aikinsu. Ya ce kungiyar ta hukunta mutum biyar da suka taka dokokinta a sassan kasar nan, kuma akwai mutum uku da ake binciken laifuffukan da ake zargin sun aikata don hukunta su.
Shugaban kungiyar na Bauchi Malam dahiru Garba, ya ce gyaran da aka yi wa ofishin zai taimaka wajen bunkasa alakar kungiyar da masu hulda da ita. Ya ce za a ci gaba da kare kayan aiki na zamani da aka samar tare da lura da wurin ta yadda za a jima ana cin moriyarsa.