Gwamnatin Bauchi za ta tsugunar da almajirai da malamansu
Gwamnatin Jihar Bauchi ta sha alwashin tsugunar da almajirai da malamansu a wuri guda a wani yunkuri na inganta rayuwarsu domin kawo karshen yawon almajiranci a jihar tare da ingana samar da ingantaccen ilimin addini. Gwamnan Jihar Malam Isa Yuguda ya bayyana haka a lokacin da yake bude ofishin Babban Daraktan Ilimin Tsangaya don lura […]
Gwamnatin Jihar Bauchi ta sha alwashin tsugunar da almajirai da malamansu a wuri guda a wani yunkuri na inganta rayuwarsu domin kawo karshen yawon almajiranci a jihar tare da ingana samar da ingantaccen ilimin addini.
Gwamnan Jihar Malam Isa Yuguda ya bayyana haka a lokacin da yake bude ofishin Babban Daraktan Ilimin Tsangaya don lura da harkokin alarammomi da limamai a karkashin jagorancin Sayyadi Ali dahiru Bauchi.
Gwamna Yuguda ya bayyana niyyar gwamnatinsa na tallafa wa alarammomi da limamai inda za a kara yawan wadanda ake ba su alawus daga mutum dubu biyar zuwa dubu goma, tare da gina makarantu da gidajen alarammomi a kananan hukumomin jihar don rage yawon almajiranci.
Gwamna Yuguda ya yaba kan gudunmawar da malamai ke bayarwa wajen ilimantarwa da kuma addu’o’in fatar alheri da zaman lafiya ga jihar da kasa baki daya.