Gwamnatin Benuwe ta sanya dokar hana fita a Katsina-Ala

A yau Litinin Gwamnatin jihar Benuwe ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a birnin Katsina-Ala da ke jihar. Rahotanni na bayyana cewa, an sanya dokar hana fitar ne saboda kaucewa aukuwar rikici a yankunan karkara da ke yankin, a jiya Lahadi ne aka yi garkuwa da mutum biyar sannan aka kashe mutum 11 […]

Gwamnatin Benuwe ta sanya dokar hana fita a Katsina-Ala

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom

A yau Litinin Gwamnatin jihar Benuwe ta sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a birnin Katsina-Ala da ke jihar.

Rahotanni na bayyana cewa, an sanya dokar hana fitar ne saboda kaucewa aukuwar rikici a yankunan karkara da ke yankin, a jiya Lahadi ne aka yi garkuwa da mutum biyar sannan aka kashe mutum 11 wanda ake zargin ‘yan tada kayar baya ne na kauyukan Ngibo da Tse-Aye a garin Ikyurav-Tiev 1cikin karamar hukumar Katsina-Ala.

‘Yan bindigar da suka kashe mutanen sun sace shanu 28 mallakin Barista Agwaza Atedze a lokacin sun kashe mutum 4 a kauyen Ngibo da kuma wasu mutum 7 a kauyen Tse Aye adadin ya kai mutum 11 da aka kashe.