Gwamnatin Birtaniya ta haramta amfani da TikTok

Gwamnatin ta ce za ta haramta amfani da manhajar saboda matsalolin tsaro.

Gwamnatin Birtaniya ta haramta amfani da TikTok

Birtaniya na shirin haramta amfani TikTok a na’urorin gwamnatinta, bayan wasu kasashen Yammacin Duniya sun dakatar da amfani da manhajar mallakar kasar China saboda dalilan tsaro.

TikTok na fuskantar karin bincike saboda fargabar cewa bayanan masu amfani manhajar mallakin kamfanin ‘ByteDance’ na Beijing na iya shiga hannun gwamnatin China, tare da lalata muradun tsaron kasashen yamma.

Cibiyar Tsaro ta Intanet ta Biritaniya, ta yi nazari kan ko ya kamata a hana amfani da TikTok daga wayoyin gwamnati, yayin da Amurka, Kanada, Belgium da Hukumar Tarayyar Turai suka dakatar da manhajar.

Ministan Ofishin Majalisar Dinkin Duniya, Oliver Dowden, ya shaida wa majalisar cewa na’urorin gwamnati za su iya shiga manhajojin wasu daga cikin jerin da aka riga aka amince da su.

“Za mu kuma hana amfani da TikTok a kan na’urorin gwamnati,” in ji shi.

Dowden ya kara da cewa haramcin bai shafi na’urori na sirri ba na takaitaccen lokaci a inda ake bukatar TikTok a kan na’urorin gwamnati saboda dalilai na aiki.

“Wannan matakin ya dace duba da takamaiman hatsarin da ke tattare da na’urorin gwamnati.”

Tun da farko, lokacin da aka ba da rahoton hasashen irin wannan haramcin, TikTok ya bayyana takaicinsa kan yadda kasashe ke haramta amfani da manhajarsa.

Majalisa ta buƙaci sojoji su kawo ƙarshen Lakurawa

Ɗan Aljeriya ya shiga hannu kan safarar makamai a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe ’yan banga sun sace mai unguwa a Kaduna

A wata 19 Tinubu ya ciyo bashin tiriliyan 50