Gwamnatin Borno na raba wa ’yan gudun hijira dabbobi 5,000

An raba awaki da tumaki 3,000 ga mata 500, sannan za a raba karin 200 kafin karshen wannan shekara

Gwamnatin Borno na raba wa ’yan gudun hijira dabbobi 5,000

Gwamnatin Borno tare da Kungiyar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya (UNDP) ta fara rabon dabbobi 5,000 ga ’yan gudun hijira a garin Pulka da ke Karamar Hukumar Gwoza ta jihar.

Babban sakataren ma’aikatar RRR, Alhaji Yusuf ya ce ma’aikatar ta raba awaki da tumaki 3,000 ga mata 500, sannan za a raba karin 200 kafin karshen wannan shekara.

Ya ce hakan wani kokari ne na dawo da al’ummomin da suka rasa muhallansu, rage radadin talauci, da ba su abin dogaro da kansu a bangaren tattalin arziki.

Da yake kaddamar da rabon, Mataimakin gwamnan jihar, Umar Usman Kadafur, ya ce wani bangare ne na shirin gwamnatin jihar na raya jihar na shekaru 25, ta hanyar tsare-tsare na shekaru 10.

Kadafur ya ce gwamnatin za ta ci gaba da amfani da dabarun inganta rayuwar al’ummar jihar, ciki har da ta hanyar hada kai da abokan huldar ci gaba domin samun kyakkyawan sakamako.

Ya kuma yi kira ga wadanda suka ci gajiyar shirin da su kula da dabbobinsu domin suna iya canza arzikinsu idan an kula da su yadda ya kamata.

Sannan ya yi alkawarin gwamnati za ta ci gaba da inganta rayuwar marasa galihu ta hannun shirin farfado da zaman lafiya da kwanciyar hankali na gwamnati.