Gwamnatin Borno ta horar da mata 162 sana’o’in dogaro da kai

Uwargidan gwamnan ta jagoranci bikin yaye ɗaliban, inda aka ba su kayan da za su fara aiki.

Gwamnatin Borno ta horar da mata 162 sana’o’in dogaro da kai

A wani mataki na ƙarfafa wa mata da ‘yan mata da dogaro da kai, uwargidan Gwamnan Jihar Borno, Dakta Falmata Zulum, ta jagoranci bikin yaye mata 162 da suka kammala horo a makarantar koyon sana’o’i da ke Bolori II, a Maiduguri.

An shirya wannan horo ne don tallafa wa mata musamman waɗanda suka yi hijira ko kuma ba su samu damar yin karatun boko ba, tare da nufin bunƙasa tattalin arziƙin jihar.

Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar, Injiniya Lawan Abba Wakilbe, ya ce shirin ya dace da manufar Gwamna Babagana Zulum, na kawar da zaman banza da bunƙasa tattalin arziƙin al’umma.

Ya kuma sanar da cewa duk ɗaliban da suka kammala horon za su samu kayan aikin da za su fara amfani da su don gudanar da sana’o’insu.

Makarantar koyon sana’o’i da tsohuwar gwamnatin marigayi Mohammed Goni, ta kafa tana bayar da horo kan sana’o’i daban-daban, irin su dinki, gyaran fuska, fenti, sana’ar kwamfuta, da sauransu.

A lokacin bikin, ɗaliban sun baje kolin basirarsu, tare da bayyana yadda horon ya taimaka musu wajen fahimtar sana’o’in da za su dogara da su.

Wakiliyar ɗaliban da aka yaye, Falmata Mohammed, ta nuna godiyarta ga gwamnatin jihar da uwargidan gwamnan bisa wannan dama da suka samu.

Hakazalika, shugabar ƙungiyar “Multi Aid Charity Initiative,” Hajiya Maryam Gimba, ta yi kira ga ɗaliban da su yi amfani da wannan horo don zama masu dogaro da kai da kuma taimakawa wajen ci gaban tattalin arziƙin jihar.

Har ila yau, an raba musu takardun shaida da kayan aikin sana’a, wanda ke nuna nasarar shirin wajen ba su damar farawa a fannin tattalin arziƙi.