Gwamnatin Borno za ta dauki malaman makaranta 5,000 aiki

Gwamnan ya ce za a dauki malaman ne da nufin rage cunkoson dalibai a makarantun jihar.

Gwamnatin Borno za ta dauki malaman makaranta 5,000 aiki

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce za a dauki malamai 5,000 aiki domin inganta ilimi musamman a makarantun firamare da sakandare a jihar.

Zulum ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Maiduguri, yayin jawabinsa na farko bayan ya rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar a karo na biyu.

“Ko da yake mun gina sabbin makarantu masu girman gaske da kuma fadada makarantun da ake da su tare da sabbin azuzuwa kusan 1,000, amma har yanzu muna fuskantar matsalolin cunkoson yara.

“Ina farin cikin sanar da cewa nan ba da jimawa ba Jihar Borno za ta fara tsarin karantun makarantun firamare da sakandare da rana.

“Zan kafa kwamitin da zai tsara hanyoyin da za a fara aiwatar da tsarin makarantun rana, kuma shi [Kwamitin] zai tantance makarantun da za a zaba daga wasu makarantunmu.”

Zulum ya bayyana cewa gabatar da karatun da rana zai haifar da karin ma’aikata kuma don haka, ya ba da umarnin daukar kwararrun ma’aikata.

Gwamnan ya kuma ce za a dauki matakan tsaro don tabbatar da nasarar makarantun da rana.

Harin Borno: Mun kashe ’yan ta’adda 34, mun rasa dakaru 6 – Sojoji

Radda ya yi wa Kwamishinoni sauyin ma’aikatu a Katsina

G-Fresh da Babiana sun nemi a saki Baɗejo

DAGA LARABA: Yadda sunayen zamani suka shafe na Hausawa