Gwamnatin Buhari alheri ce ga ’yan Najeriya – Sanata Adamu

Tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa kuma Sanatan Nasarawa ta Yamma Alhaji Abdullhi Adamu ya ce gwamnatin Buhari alheri ce ga dukkan ’yan Najeriya, inda a shekara guda da zuwanta ta samar da fa’idojin da suka fi na shekara shida na tsohuwar gwamnatin Jonathan. Alhaji Abdullahi Adamu ya bayyana haka ne lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa kan […]

Gwamnatin Buhari alheri ce ga ’yan Najeriya – Sanata Adamu

Sanata Abdullahi AdamuTsohon Gwamnan Jihar Nasarawa kuma Sanatan Nasarawa ta Yamma Alhaji Abdullhi Adamu ya ce gwamnatin Buhari alheri ce ga dukkan ’yan Najeriya, inda a shekara guda da zuwanta ta samar da fa’idojin da suka fi na shekara shida na tsohuwar gwamnatin Jonathan.
 Alhaji Abdullahi Adamu ya bayyana haka ne lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa kan cikar gwamnatin Buhari shekara daya a gadon mulki a garin Keffi, inda ya ce kowa ya san cewa an samu ci gaba masamman a bangaren tsaro da kuma yaki da cin hanci da rashawa. Ya ce yanzu haka azzaluman mutane da dama na tsoron sata ko almundahana da dukiyar al’umma, “Saboda wannan gwamnati ce da ta zo da tsarin kwato dukiyar kasa ta yadda talakawa za su amfana da ita, don haka duk mai hankali na da hujjar cewa gwamnatin Buhari ta zo da alheri,” inji shi.
Shi ma da yake tsokaci kan batun, Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa Honorabul Silas Ali Agara ya ce, “Yawan buri da rashin hakuri ke sa wasu ganin kamar wannan gwamnati ta gaza. Amma babu shakka kudirorin gwamnatin masu kyau ne ga masu hankali da lura.
Shi kuwa Kwamshinan Kimiyya da kere-kere da kuma Ilimi na Musamman na Jihar Nasarawa Injiya Idris Mohammed ya shawarci jama’a ne su rage burorin ga gwamnati domin gyara abu ne mai wuya ba kamar barna ba. Ya ce gwamnatin ta gaji kura-kurai da dama, kuma wannan ne ya sa wadansu ke ganin kamar gwamnatin ba ta kokari, alhali tana kokari matuka domin share wa duk ’yan Najeriya hawaye. Kuma mulki kamar gona ne da ba a shuka yau a girbe yau, sai an sha wuya an jure kafin a ji dadi.
Injiniya Wada Mohammed Yahaya Adamus, mai bai wa Gwamnan Jihar Nasarwa Shawara a kan Ayyuka, ya ce hauhawar kayan abinci da na masarufi insha Allahu abu ne na karamin lokaci, saboda kayan sun tashi ne sanadiyar faduwar farashin man fetur, don haka ba laifin gwamanti Najeriya ba ne.
Shugaban Jam’iyyar APC na karamar Hukumar Keffi Alhaji Suleiman Y. Garba Maicarbi, ya ce kiyayya ga wannan gwamnatin rashin adalci ne domin wannan gwamnatin ta zo da fa’idoji da dama masamman a bangaren tsaro da adalci.
Sai dai Shugaban Jam’iyyar PDP Alhaji Mohammed Aliyu Babayo ya ce gwamnatin ta zo da kura-kurai da yawa da ’yan alheran da ba a rasa ba a bangaren tsaro da yaki da cin hanci da rashawa. Ya ce gwamnatin ta sanya al’umma cikin matsanancin talauci wanda babu wanda ya san karshensa, kuma kowa ya san talauci kan iya sanya mutum a cikin kowane irin mumunan hali don haka gwamnatin ta zamo matsala ga ’yan Najeriya.