Gwamnatin Buhari kamar motar ’yan gada-gada ne – Fayose

Gwamnan Jihar Ekiti Mista Ayodele Fayose ya sake caccakar Shugaban kasa ýMuhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC, inda ya ce sun damfari ’yan Najeriya da romon baka har suka zabe su, tare da bayyana gwamnatin Buhari da cewa kamar motar ’yan gada-gada ce.Gwamna Fayose ya fadi tab akin kakakinsa, Lere Olayinka cewa, “Duk abin da […]

Gwamnatin Buhari kamar motar ’yan gada-gada ne – Fayose
Gwamnatin Buhari kamar motar ’yan gada-gada ne – Fayose

Gwamnan Jihar Ekiti Mista Ayodele Fayose ya sake caccakar Shugaban kasa ýMuhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta APC, inda ya ce sun damfari ’yan Najeriya da romon baka har suka zabe su, tare da bayyana gwamnatin Buhari da cewa kamar motar ’yan gada-gada ce.
Gwamna Fayose ya fadi tab akin kakakinsa, Lere Olayinka cewa, “Duk abin da Buhari da jam’iyyarsa suka yi alkawari ga ’yan Najeriya lokacin da suke neman kuri’a sun dawo suna musantawa, don haka baa bin mamaki ba ne wata rana Buhari ya fito ya ce ba a karkashin Jam’iyyar APC aka zabe shi ba.”
 Gwamna Fayose ya bayyana cewa da’awar da Buhari ya yi cewa bai yi alkawarin ba marasa aiki alawus din Naira dubu biyar-biyar ba da kuma bayanin da Minista Labarai, Alhaji Lai Mohammed cewa APC ba ta yi alkawarin kirkiro da ayyukan yi miliyan uku a duk shekara bad a gagarumar damfara ta siyasa da Shugaban kasar da jam’iyyarsa suka yi.
Ya ce: “Ba su cika ko daya daga cikin alkawuran da suka yi ga ’yan Najeriya ba, maimakon haka sun gaya mana cewa ba su yi kowane alkwari ba. Kusan shekara guda ke nan da Buhari ya karbi mulki babu ko aiki daya da ya samar. Maimakon samar da aikin yi miliyan uku da suka yi alkwari, abin da muke gani shi ne rasa ayyukan yi da kuncin tattalin arziki da aringizon kasafin kudi.”
Fayose ya ce wani abin damuwa Shugaba Buhari ya fi zabar kasar waje don furta muhimman maganganun da suka shafi kasa, indas ya yi tambayar ko Buhari ya zama dan Najeriya mazaunin kasar waje ne ko Shugaba na kafar sadarwar zamani.
Sai ya zargi Shugaba Buhari da kokarin musuluntar da Najeriya ta hanyar nuna goyon baya ga Falasdinu tare da bayyana Falasdinawa a matsayin ’yan uwansa day a wajaba su samu kasarsu.
Ya ce; “Duk da ni masoyin Musulmi ne, ina mu’amala da su kamar yadda nake yi da Kiristoci a jihad a sassan kasar nan, amma wajibi ne Najeriya ta zama marar addini da ‘’yan kasar za su rika ambaton Yesu Almasihu da Allah (Subhanahu Wa Ta’ala) cikin ’yanci.”
Gwamnan ya ce tun da Shugaba Buhari ya musanta takardun kamfe dinsa mai suna “Alkawarina da ’Yan Najeriya,” da aka yada ga ’yan Najeriya a lokacin kamfe kuma aka buga a wasu jaridun kasa tare da watsa su a Intanet a ranakun 16 da 17 ga Maris din bara, ya san an damfari ’yan Najeriya.
 “Yanzu ’yan Najeriya sun fahimci sun shiga “Motar ’Yan Gada-Gada,” saboda Buhari da APC sun musanta dukkan alkawuran da suka yi lokacin kamfe ta hanyar musanta takardun kamfe dinsu.”
Sai dai Sanata Kashamu Buruji na Jam’iyyar PDP daga Jihar Oyo ya bukaci masu sukar Shugaba Buhari su guji suka marar ma’ana.
Sanata Kashamu, ya ce maimakon yunkurin rusa gwamnatin Buhari, ya kamata ne a rika suka mai ma’ana ga gwamnatinsa ba tare da cin mutunci ba. Sanatan ya fadi haka ne a garin Ijebu-Igbo lokacin kaddamar da shirin bayar da tallafi. Ya ce Shugaba Buhari yana kokari sosai. Kuma idan ana ganin kamar akwai tafiyar hawainiya ce to wannan bai rasa nasaba da rashin kudi da kuma kokarin da ake yi na toshe hanyoyin sace kudaden.
“Kada ’yan Najeriya su yarda ’yan siyasa su rika yaudararsu. Mukan sanya siyasa a cikin komai. Mun manta cewa an gama kamfe da zabe, yanzu muna da gwamnati a kasa don haka wajibi ne mu yi watsi da son zuciya da adawar siyasa mu hada hannu wajen gina kasarmu ta hanyar bayar da shawarwari masu ma’ana kamar yadda wasu manyan kasa irin su Farfesa Wole Soyinka da Cif Emeka Anyaoku suke yi. Ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya,” inji Sanatan.