Gwamnatin Buhari: Mulki dai iyakarsa nan duniya —Zakzaky
Ba suna so su kashe ni ba ne, to ga fili ga mai doki.
Shugaban Kungiyar Musulmai ta Mabiya Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ya ce duk wani mulki ko gwamnati iyakar ita ce nan duniya.
A hirarsa ta farko da ya yi da wata kafar yada labarai ta Hausa tun bayan da ya shaki iskar ’yanci, Zakzaky ya fadi hakan ne a matsayin martani dangane da zargin da Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kaduna suka yi a kansa da ya kai ga an tsare shi har tsawon shekaru shida.
Fiye da shekara shida kenan tun bayan rikici tsakanin mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da sojojin Najeriya, bisa zargin da sojoji suka yi na cewa mabiya El-Zakzaky sun tare musu hanya a Zaria.
A karshen shekarar 2015 ce aka kama Sheikh Zakzaky bayan mabiyansa sun yi wata mummunar arangama da dakarun sojin Najeriya a garin Zariya da ke Jihar Kaduna.
Wannan takaddama ce ta kai ga an cafke malamin tare da matarsa Zeenatu.
Sai dai a watan Yulin 2021 ne wata Babbar Kotu a Jihar Kaduna karkashin jagorancin Mai Shari’a Kurada, ta bayar da umarnin a saki Sheikh El-Zakzaky da mai dakinsa, inda ta wanke su daga dukkan zargin da ake yi musu bayan kwashe kimanin shekara shida a tsare.
A cikin wata tattaunawa da Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya yi da Sashen Hausa na BBC, Sheikh Zakzaku ya ce “mulki dai iyakarsa nan duniya.
“Kwana nawa ne mulkin ai zai zo ya kare. Ita ma rayuwar za ta zo ta kare ai lokacin da aka harbe ni wani Minista cikin Ministocin Buharin ya bugo min waya, na amsa an harbe ni ina kwance.
“Na ce masa ka ga abin da gwamnatinku ta yi min ko? Na ce masa ka ce ina gaida Janar Buhari, ku yi gwamnati lafiya, sai mun hadu a lahira.
“Duk abin da za ku yi ku yi za mu tsaya a gaban Allah ranar gobe kiyama. Kuma kiyamar ba nisa gare ta ba.”
Dangane da lokacin da jamian tsaro suka je kama shi, Sheikh Zakzaky ya ce bai yi fargabar ko watakila za su kashe shi ba, “don akwai wanda ya ce min ko zan sauya muhalli?
“Na ce Allah Ya sauwake, ba yadda za a yi an zo kashe ni kuma na tafi wani waje bayan kuma an kashe mutane kafin ni.
“Don haka su zo su cim ma burinsu illa iyaka ke nan su kashe ni, ina jiran kisan ne ba wani abu ba.
Kazalika, Sheikh Zakzaky harbinsa da aka yi da kuma kona gidansa da aka yi umarni ne na shugaban kasa.
“Shugaban Kasa shi da kansa ne ya ba da umarnin hakan daga Kaduna. Sai da aka ba shi tabbacin an kona gidana da ni da matata da ’ya’yana.
Zakzaky, ya kara da cewa, da za su hadu da Buhari da Gwamna Nasiru El-Rufa’i na Kaduna zai ce musu su kammala ayyukan da suka fara, su ci gaba su cikata ladansu.
“Ba suna so su kashe ni ba ne, to ga fili ga mai doki.”
Dangane da komawarsa Zariya, Sheikh Zakzaky ya ce “Da Yardar Allah ba abin da zai hana ni duk da abubuwan da suka faru a baya, nan gaba zan koma na gina muhallina da makaranta da sauran su.
“Amma da yake yanzu abin da yake gabanmu shi ne lafiyar jikinmu, amma in shaa Allah duk abin da muka rasa a Zariya za mu mayar da su kuma duk abin da ake yi za a ci gaba da yi,” a cewar Sheikh Zakzaky.
Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, wanda ya yi sama da shekara shida ke nan a tsare tun bayan rikici tsakanin mabiyansa da sojojin Najeriya, bisa zargin da sojoji suka yi na cewa mabiya El-Zakzaki sun tare musu hanya a Zariya.