Gwamnatin Buhari ta gaji munanan matsaloli – Sheikh Sa’idu Jingir
Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Biyu na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya bayyana halin da mutanen kasar nan suke ciki na wahala da cewa bakin gado ne da gwamnatin ta iske kanta a ciki ya jefa jama’a cikin ni-’yasu. “Mummunan gadon da gwamnatin Shugaba Buhari ta […]
Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na Biyu na kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta kasa, Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya bayyana halin da mutanen kasar nan suke ciki na wahala da cewa bakin gado ne da gwamnatin ta iske kanta a ciki ya jefa jama’a cikin ni-’yasu.
“Mummunan gadon da gwamnatin Shugaba Buhari ta yi ne ya jefa kasar nan cikin mawuyacin halin da ake yanzu, gwamnatin da ta gabata ta yi barnar da Allah ne Ya san adadinta, Shi ne Ya taimake mu Ya kawo mana canji domin fitar da kasar nan daga kwazazzabon da ta fada. Dole wannan gwamnati ta rufe bakin aljihu domin daidaita al’amuran kasa,” inji Malamin.
Sheikh Sa’idu Jingir ya yi wadannan kalamai ne a Sakkwato a ci gaba da gudanar da tafsirin Ramadan na bana da kungiyar ta turo shi, inda ya ce yana goyon bayan maganar da Mai alfarma Sarkin Musulmi ya yi ta a bude iyakokin kasa domin shigowa da abinci. Ya ce “Dokar da gwamnati ta yi mai kyau ce domin za ta kara farfado da arzikin kasa, amma in an ciza a hura, ya kamata a sanya ka’idojin shigowa da shinkafa marasa tsanani a sassauta lamuran nan halin da ake ciki ba dadi, bude iyakoki zai zama alheri, gwamnati za ta samu kudin shiga, talaka zai samu sauki.”
Sheikh Sa’idu Jingir ya ce “Duk hukuncin da Allah Ya ce a aiwatar, ba talaka ake nufi ya zartar da shi ba, duk wanda ya zagi Annabi (SAW) kashe shi za a yi ta hanyar alkali, in ba a yi haka ba za a fito da abin da zai sanya a yi kuren da mutanen suka yi a kwanan baya, ba su kai kotu ba suka zartar da hukunci da kansu. Ina kira ga malamai su ji tsoron Allah su cire kwadayi a zukatansu, Musulmi da Kiristoci, malamai a cikin al’umma kamar ruwa ne su fada wa shugabanni gaskiya wannan lalacewar ’yan siyasarmu domin malamai sun lalacen