Gwamnatin Buhari ta gurgunta tattalin arzikin Najeriya — Sanusi
Wasu shafaffu da mai ne suka yi wa tattalin arzikin kasar nan kamshin mutuwa.
Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II, ya ce tsohuwar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gurgunta tattalin arziki ba tare da neman shawarar kwararru ba.
Sarki Sanusi wanda kuma shi ne tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya bayyana hakan a wani sakon bidiyo da ya aike wa ‘yan Najeriya ta yanar gizo.
- Wasu ’yan siyasa na kokarin shirya wa gwamnatin Tinubu mummunar zanga-zanga – DSS
- Magidantan da ’yan bindiga suka kashe a masallaci a Kaduna sun bar marayu 61
Ya bayyana cewa wasu sun ribaci rikon sakainar kashi da aka yi wa tattalin arzikin da har aka samu “wani yaro mara ilimi” ya mallaki jirgin sama a karkashin gwamnatin da ta shude
Ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi hakuri da wannan gwamnati da shugaba Bola Tinubu ke jagoranta, yana mai cewa gwamnatin baya ce ta gurgunta komai.
Sanusi ya bayyana cewa ya an sha samun masu rubuto masa takarda suna neman ya yi magana kan halin da kasar nan ke ciki.
Sai dai ya ce wannan ba lokaci ba ne da ya kamata ya yi magana kan matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
“Shekara takwas da ta wuce, Najeriya ta yi rayuwar karya, gwamnati ta ciyo bashi daga ciki da wajen kasar nan. Kimanin Naira Tiriliyan 30 aka karbo daga Babban Bankin Kasar.
“Duk kudaden shiga da kasar nan ta samu a cikin ’yan shekarun da suka gabata ba za a iya biyan bashi ba. Bashin ya wuce kashi 100.
“Wadanda suka rubuta takarda, suna neman mu yi magana kan halin da kasar nan ke ciki; amma bai dace in yi magana a yanzu ba.
“Kamar direban da ke kan hanya yana tuki da ganganci ne ka ja hankalinsa game da rami a gaba bai saurare ka ba. Me za ka fada masa bayan motar ta fada cikin rami?
“Mutane sun ki sauraron mu a lokacin. Yanzu za mu ba su shawara kawai su yi hakuri. Ba zan taba cewa Tinubu ya ingiza Najeriya cikin wahala ba. Ba wai ba shi da aibu ba ne.
“Idan sun kara haraji, dole ne mu biya tun da rancen kudi ba zai yiwu ba. Idan CBN ya buga karin takardun Naira, dala za ta kai N1,500. Dole ne mu sha wahala. Lokacin da nake Gwamnan CBN duk dala daya ana canjar da ita N150 ne. A yau kuwa ta kai kusan N900.
“Sun yi wa tattalin arzikin abin da suke so kuma sun ki sauraron masana.
“A cikin shekara takwas da ta gabata kawai shafaffu da mai sun sayi dala a kan N400 sannan suka sayar da N540.
“Akwai yaron da ba shi da gogewa kuma wanda bai taba yin aiki a ko ina ba ya mallaki jirgin sama mai zaman kansa.”