‘Gwamnatin Buhari ta samu nasara kan zaman lafiya’
Sarkin Tilden Fulani kuma Hakimin Tilden Fulani da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi Alhaji Aliyu Muhammad Tukur ya ce a cikin kwana 100 da gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari ta yi a mulkin kasar nan, ta samu gagarumar nasarawajen samar da zaman lafiya a kasar nan. Alhaji Aliyu Tukur ya bayyana haka ne a […]
Sarkin Tilden Fulani kuma Hakimin Tilden Fulani da ke karamar Hukumar Toro a Jihar Bauchi Alhaji Aliyu Muhammad Tukur ya ce a cikin kwana 100 da gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari ta yi a mulkin kasar nan, ta samu gagarumar nasara
wajen samar da zaman lafiya a kasar nan. Alhaji Aliyu Tukur ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce “Babbar nasarar da gwamnatin Buhari ta samu a cikin kwana 100 na mulkinta shi ne zaman lafiya. Domin al’ummar Najeriya sun ga canji kan zaman lafiya.”
Ya ce “Kafin zuwan wannan gwamnati, kowa yana zaman dar-dar ne, amma yanzu wannan ta kau. Duk inda masu aikata laifi
suke kowa ya fara shafa wa kansa ruwa. Hare-haren bama-bamai da ake kaiwa a da, yanzu sun yi baya.”
Ya ce gwamnatin ta samu nasarar inganta samar da wutar lantarki saboda, a baya sai a yi kwana uku babu wuta, amma a yanzu akan yi awa 13 ba a dauke wuta ba.
Hakimi ya kuma ce yanzu ma’aikatan gwamnati sun shiga taitayinsu aiki ya fara tafiya yadda ake bukata. Kuma ga man fetur ya samu a gidajen mai kan farashin gwamnati na Naira 87.
Sai kuma ya kawo misali da kokarin da gwamnatin take yi wajen karbo kudin jama’ar kasar nan da aka sace.