Gwamnatin Buhari tana kokarin farfado da martabar Najeriya – Abdulhamid Rimi

Aminiya: Ciyaman yaya kake kallon salon  gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma manufofinta?Abdulhamid Rimi: To, a  ganina salon mulkin Shugaba Muhammadu Buhari yana da kyau, idan aka dubi irin mulkin da aka yi wa kasar nan na tsawon lokaci cikin barna. Duk dan Najeriya ya yarda cewa wannan gwamnati ta Buhari ta karbi mulki ne […]

Gwamnatin Buhari tana kokarin farfado da martabar Najeriya – Abdulhamid Rimi
Gwamnatin Buhari tana kokarin farfado da martabar Najeriya – Abdulhamid Rimi

Aminiya: Ciyaman yaya kake kallon salon  gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma manufofinta?
Abdulhamid Rimi: To, a  ganina salon mulkin Shugaba Muhammadu Buhari yana da kyau, idan aka dubi irin mulkin da aka yi wa kasar nan na tsawon lokaci cikin barna. Duk dan Najeriya ya yarda cewa wannan gwamnati ta Buhari ta karbi mulki ne a lokacin da kasar nan tamu ta shiga cikin wani mawuyacin hali wanda dole sai an dauki matakai masu kwari domin yin gyare-gyare da farfado da darajar kasar. Don haka gaskiya wannan gwamnati tana kokari wajen yin tsarin da zai taimaka a cimma nasara musamman ta fuskar tsaro da tattalin arziki da kuma samar da yanayi mai kyau na inganta rayuwar al’ummar kasar nan kamar yadda tsarin mulkin dimokuradiyya ya nuna. Sai dai ina fata ’yan uwana ’yan Najeriya za mu hadu mu ci gaba da bai wa gwamnatocinmu goyon baya da hadin kai ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.
Aminiya: Al’amarin tsaro abu ne mai matukar muhimmanci, me za ka ce game da yadda yanayin tsaro yake kasancewa a halin yanzu a kasar nan?
Abdulhamid Rimi: Gaskiya an yi fama da tabarbarewar tsaro a wannan kasa tamu da kuma rashin kwanciyar hankali, amma idan ka dubi yadda abin yake a halin yanzu za mu ga cewa ana samun nasarori ingantattu ta fuskar tsaro da zaman lafiya. Don haka wannan babu abin da za mu ce sai godiya ga  Allah  tare da fatan alheri ga shugabanninmu da kuma hukumomin tsaro wadanda suke aiki dare da rana domin tabbatar da cewa komai ya zamo tarihi. Haka kuma mu kanmu ’yan Najeriya sai mu kara godiya ga Allah Wanda Shi ne Ya kawo mana dauki cikin ikonSa har muka samu canji a kasa ba tare da an samu wata matsala ba.
Amniya: Amma kuma jama’a suna kokawa cewa gwamnatin Buhari ta tsayar da komai kuma ana cikin matsin rayuwa, bayan canjin da aka samu, mene ne ra’ayinka kan wannan batu?
Abdulhamid Rimi:  To, ai kowa dai ya san cewa barna ce ake iya yi lokaci guda, amma gyara sai a hankali. Don haka ina kara yin kira ga al’ummar kasar nan su kara hakuri tare da nuna juriya, da yardar  Allah komai zai daidaita. Kuma kasa za ta kara samun ci gaba musamman a fannin tattalin arziki da tsaro da kuma dogaro da kai. Mai girma Shugaban Muhammadu Buhari jagora ne mai kishin kasar nan da al’ummarta, don haka mu kara yi masa kyakkyawan zato cewa gwamnatinsa za ta yi aiki wajen inganta rayuwar al’ummar birane da karkara. Yana da kyau mutane su fahimci cewa wannan halin da ke ciki ba Shugaba Buhari ne ya kawo shi  ba, kuma ba gwamnatin sa ba ce  ta kawo. Abu ne da ya zo ya iske an jagwalgwala kasar, sai mu nemi taimako daga Allah wajen ganin bayan hakan, kuma in sha Allahu nan gaba kadan za mu hadu mu yi murna da farin cikin cewa yau Najeriya tana sahun gaba wajen ci gaba ta kowane fanni. Sannan mu kara kasancewa masu kishin kasa da son ci gabanta, kada mu rika yi wa gwamnatocinmu zagon kasa da warware tufkar da ake yi.
Aminiya: Idan muka koma batun Jihar Kano, a kwanakin baya ne gwamnatin jihar ta yi wa wasu barayin shanu afuwa, tare da kokarin dora su a kan hanyoyi sahihai domin su dogara da kansu, yaya ka dubi wannan afuwa da gwamnati ta yi?
Abdulhamid Rimi: Babu shakka wannan mataki da Mai girma Gwamnan Jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya dauka ya yi kyau kwarai da gaske, kuma al’umma na ciki da wajen jihar ta Kano sun yaba sosai. Haka kuma su kansu wadanda suka amfana da afuwar sun yarda cewa al’umma ba sa jin dadin abubuwan da suka yi na satar shanu. Don haka ina fata Allah Ya sa wannan mataki da Gwamna ya dauka zai zamo wata hanya ta samar da wata masalaha ingantacciya ga al’amarin satar shanu da sauran laifuffuka a fadin Jihar Kano da kuma kasa baki daya. Sannnan ina jinjina wa hukumomin tsaro da sauran jama’a masu son zaman lafiya da kwanciyar hankali bisa kokarin da suke yi wajen ganin ana samun zaman lafiya da kaunar juna. Kuma ina taya wadanda suka amfana da wannan afuwa murnar shiga cikin sabuwar rayuwa mai albarka.
Aminiya: Kwanaki wata kungiya ta ba ka lambar yabo saboda gudummawar da kake bayarwa wajen samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a karamar Hukumar Sumaila da Jihar Kano, yaya ka dauki wannan karramawa?
Abdulhamid Rimi: Duk wanda aka zakulo aka karrama da lambar yabo zai ji dadi kuma zai kara himma kan abin da yake yi na inganta al’amura a duk inda ya tsinci kansa. Saboda haka wannan yabo da Allah Ya sa na samu ya kara min kwarin gwiwa tare da zimmar ci gaba da aikin kyautata rayuwar al’ummar karamar hukumarmu ta Sumaila. Sannan ina godiya ga waccan kungiya da ta karrama ni da kuma su kansu al’ummar karamar Hukumar Sumaila wadanda suke bai wa majalisar karamar hukuma goyon baya da fatan alheri.
Aminiya: Mene ne sakonka ga ’yan Najeriya?
Abdulhamid Rimi: Kafin isar da sakona zan yi amfani da wannan dama wajen yin godiya ta musamman ga Mai girma Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje saboda kyawawan matakan da yake dauka na inganta rayuwar al’ummar jihar. Sannan ina godewa Majalisar Dokokin Jihar bisa hadin kai da ake samu tsakanin majalisa da bangaren zartarwa, hakan abin alfahari ne musamman a tsari irin na dimokuradiyya. A karshe ina kara yin kira ga ’yan Najeriya mu kasance masu kishin kasa da kaunar zaman lafiya ta yadda shugabanni za su samu ikon gudanar da manufofin gwamnatocinsu. Allah Ya kara mana lafiya da  zama lafiya da kuma karuwar arziki a kasar nan.