‘Gwamnatin Buhari za ta dawo da martabar kasar nan’
Shugaban karamar Hukumar Kura a Jihar Kano Alhaji Basiru Abubakar Turaki ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari za ta dawo da martabar kasar nan duk da cewa Najeriya ta dade cikin tabarbarewar da yin gyara sai an yi hakuri kafin a cimma nasarar da ake bukata. Alhaji Basiru Abubakar Turaki ya bayyana haka ne yayin ganawarsa […]
Shugaban karamar Hukumar Kura a Jihar Kano Alhaji Basiru Abubakar Turaki ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari za ta dawo da martabar kasar nan duk da cewa Najeriya ta dade cikin tabarbarewar da yin gyara sai an yi hakuri kafin a cimma nasarar da ake bukata.
Alhaji Basiru Abubakar Turaki ya bayyana haka ne yayin ganawarsa da manema labarai a Kano, inda ya ce sabon Shugaban kasa mutum ne mai gaskiya da rikon amana, kuma zai sanya sahihan mutane cikin gwamnatinsa domin su taimaka masa wajen tafiyar da shugabancin Najeriya.
Sai ya yi kira ga ’yan Najeriya su taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari da addu’o’in samun nasara a wannan lokaci da kowa ke fatan samun sauyi a rayuwa.
Alhaji Basiru Turaki ya ce ’yan Najeriya suna son kasar nan ta kasance cikin zaman lafiya da hadin kai, don haka wajibi ne a kaunaci juna a zauna lafiya ta yadda za a cimma nasarar bunkasa kasar.
Ya yi fatan alheri ga sabon Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje da Mataimakinsa Farfesa Hafiz Abubakar, tare da yin kira ga al’ummar jihar su ba sabuwar gwamnatin hadin kai ta yadda za ta samu damar aiwatar da kyawawan manufofinta.