Gwamnatin dankwambo ta kashe fiye da Naira biliyan bakwai kan ilimi – Kwamishina
Kwamishinar Ilimi ta Jihar Gombe Hajiya Nana A’ishatu MB Ahmad, ta ce gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo, ta fi ba ilimi fifiko, inda a cikin shekara uku na mulkinsa ta kashe fiye da Naira biliyan bakwai ga ci gaban ilimi a jihar.Hajiya Nana A’ishatu, ta ce tun hawan Gwamna dankwambo karagar mulki […]

Kwamishinar Ilimi ta Jihar Gombe Hajiya Nana A’ishatu MB Ahmad, ta ce gwamnatin jihar a karkashin Gwamna Ibrahim Hassan dankwambo, ta fi ba ilimi fifiko, inda a cikin shekara uku na mulkinsa ta kashe fiye da Naira biliyan bakwai ga ci gaban ilimi a jihar.
Hajiya Nana A’ishatu, ta ce tun hawan Gwamna dankwambo karagar mulki a shekarar 2011 ya shaida wa jama’ar jihar cewa akwai babban kalubale a bangaren ilimin wanda shi ne tushen rayuwar kowane dan Adam.
Kamar yadda ta ce a duk inda Gwamnan yake magana cewa yake abin alfaharinsa na daya shi ne ilimi, na biyu ilimi na uku ilimi, shi ya sa daga hawansa zuwa yanzu ya raya ilimi sosai a jihar.
Ta ce fiye da makaarantun firamare da sakandare 50 ne Gwamna dankwambo ya sake musu fasali a fadin jihar inda wasu aka yi musu kwaskwarima wasu kuma aka gina sababbi, kuma duk firamaren an maida su bene hawa daya.
Kwamishina ta ce Gwamna dankwambo bai tsaya haka ba, ya gina Kwalejin Ilimi ta jiha a garin billiri, kuma ya samar da filin aka fara gina Kwalejin Kimiyya da kere-kere (Polytechnic) a garin Bajoga, ga kuma Kwalejin Koyon Aikin Shari’a a garin Nafada.
“Na yi Kwamishinar Ilimi na shekara hudu a gwamnatin da ta shude ta Alhaji Muhammad danjuma Goje, amma kwata-kwata a babban aiki na jihar bai wuce Naira biliyan daya ba ya kashe a harkar ilimi a shekarunsa na farko, amma yanzu dankwambo a shekara uku ya kashe fiye da Naira biliyan bakwai,” inji ta.
Ta ce Gwamna dankwambo ya gina makarantun allo biyar a jihar inda kowace aka gina mata ajujuwan karatu bene da wuraren kwanan dalibai da gidajen alarammominsu da ban-dakuna masu kyau, kuma idan suka gama karatunsu za su samu takardar shaida.
Hajiya A’ishatu, ta ce karatun boko da aka shigar a makarantun ba zai shafi karatunsu na allo ba, kari ne da zai taimaka musu wajen yin aikin gwamnati idan suna so, ko su shiga makarantun gaba don zurfafafa iliminsu.