Gwamnatin Edo ta fara jigilar mabarata zuwa yankunansu na asali
Gwamnatin Jihar Edo a shirinta na kakkabe mabarata da tsaftace jihar ta fara kwasar daruruwan mabarata da suka hada da mata da yara har da sarkin makafi, Alhaji Ahmadu Gwaram da iyalinsa tare da guragu zuwa yankunansu na asali. Motocin bas-bas na Kamfanin Magorawa guda biyar ne suka fara tashi da kashi na farko na […]
Gwamnatin Jihar Edo a shirinta na kakkabe mabarata da tsaftace jihar ta fara kwasar daruruwan mabarata da suka hada da mata da yara har da sarkin makafi, Alhaji Ahmadu Gwaram da iyalinsa tare da guragu zuwa yankunansu na asali.
Motocin bas-bas na Kamfanin Magorawa guda biyar ne suka fara tashi da kashi na farko na wadannan mabaratan zuwa Kano da misalin karfe hudu da rabi na yammacin ranar Lahadi da ta gabata.
Madam Blessing Maigida, Kwamishinar Hukumar kula da sha’anin harkar mata da yara ta jihar ba ta yarda ta yi wa ’yan jarida wani bayani ba, domin ta ce ba a ba ta izini ta yi magana da ’yan jarida game da kwasar mabaratan da gwamnatin jihar ta fara aiwatarwa zuwa ta maida su yankunan da suka fito ba amma kuma wani ma’aikaci mai aiki da hukumar wanda ya ce kada a fadi sunansa ya shaida wa Aminiya cewa ana sa rai gwamnatin za ta ci gaba da kwasar sauran mabaratan da suka boye kansu a cikin garin Benin da kewayanta ta kai su garuruwansu domin tabbatar da ba ta nuna bambanci ba a cikin ayyukanta na tsaftace jihar.
A yayin da ake fama da tattara wadannan mabaratan tare da hana ’yan jarida daukar hoto ko ganawa da su, a ranar Lahadi da ta gabata, wakilin Aminiya a sirrance ya samu daukar hotunan wasu daga cikin yaran da mata da aka tara su a harabar ofishin hukumar kuma ya zanta da wasu mata makafi, kafin a zo a tattara su a sa su a motocin jigilarsu a tafi da su.
Malama Adama matar Alhaji Ahmadu Gwaram sarkin makafi Benin, ta ce: “Mu dai zamanmu a wannan garin Benin kusan shekaru hamsin amma ba mu taba mu fuskanci tashin hankali ba sai a wannan karon, don haka muna rokon gwamnatin jihar nan ta taimaka ta bar mu mu ci gaba da rayuwarmu a nan Benin. Idan kumaa hakan bai yi ba to fatana ita ce gwamnatocin Arewa su taimake mu da abin da ya dace ga rayuwarmu ta nakasassu.”
A’isha Muhammad, matar wani makaho, ta ba da shawara kamar haka, inda ta ce: “Shawarata ga wannan gwamnatin ta yi hakuri ta tantance ta raba mu da wadannan baragurbin, ta mai da su jihohinsu, domin ina ganin ba daidai ba ne a ce laifin wani yana shafar wani da bai san hawa da sauka ba. Su kuma wadannan matan su ji tsoron Allah su gyara halayensu daga nan har Arewan.”
Malama Sahura Muhammad tana cewa: “Mun dade muna zaman lafiya a Benin, don haka ’yan uwanmu mata lafiyayyu da suka baro gidajen mazajensu suka debo yara kanana suka shiga da su kurmi, su ne suka jawo mana duk wannan abin da ya faru; domin kuma sarkinmu na makafi ya yi iyakacin kokarinsa amma sun nuna sun fi karfinsa.”
Adama Ahmadi kuwa cewa ta yi: “Mu dai abu ya fi karfinmu sai mu yi tawakkali ga Allah, domin gaba dayanmu mu matan makafi a nan Benin muna son gwamnatin jihar ta bar mu tare da mazajenmu, mu ci gaba da zamanmu lafiya, muna samun abin rufin asiri babu fallasa, wadanda suka janyo mana wannan a debe su a maida su garuruwansu; su koma gidajen mazansu na aure.”
Adama Gwaranjawa danbatta ta ce: “Ina kira ga gwamnatocin jihohinmu na Arewa su yi wa Allah su taimake mu da sana’ar da za mu iya dogaro da kanmu.”
Wata yarinya ’yar shekara 13 mai suna Uzaira Salihu ta shawarci iyayen irin wadannan yara da wasu matan suke rabawa da iyayensu cewa su sa yaran makaranta. “Abin da na gani ya dace a yi shi ne, masu ido lafiyayyu a maida su Arewa, a ba su sana’ar da za su yi; su kuma wadannan yaran a kai su wurin iyayensu su sa su makarantar addini da na zamani; domin su samu su girma da kyakkyawar tarbiyya.”