Gwamnatin Filato ba ta yi wa Hausawa da Fulanin yankin Bassa adalci ba – Ya’u PJ

Garkuwar al’ummar Hausawa da Fulani na yankin Pengana da ke karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato Alhaji Ya’u Bala PJ ya ce gwamnatin jihar a karkashin Jam’iyyar APC ba ta yi wa Hausawa da Fulani karamar hukumar adalci ba, inda ba ta dauki ko mutum daya daga cikinsu ta tsarma a cikin shugabannin riko na […]

Gwamnatin Filato ba ta yi wa Hausawa da Fulanin yankin Bassa adalci ba – Ya’u PJ
Gwamnatin Filato ba ta yi wa Hausawa da Fulanin yankin Bassa adalci ba – Ya’u PJ

Garkuwar al’ummar Hausawa da Fulani na yankin Pengana da ke karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato Alhaji Ya’u Bala PJ ya ce gwamnatin jihar a karkashin Jam’iyyar APC ba ta yi wa Hausawa da Fulani karamar hukumar adalci ba, inda ba ta dauki ko mutum daya daga cikinsu ta tsarma a cikin shugabannin riko na karamar hukumar ba.
Alhaji Ya’u Bala PJ ya ce duk da cewa al’ummar Hausawa da Fulani ne suka fi zaben Jam’iyyar APC a karamar hukumar a zabubbukan da suka gabata, inda suka fito kwansu da kwarkwatarsu daga sama har kasa, amma da aka zo nada shugabannin riko mai mutum bakwai a karamar hukumar tun daga shugaba da sakatare da kansiloli guda biyar, sai aka ki daukar ko mutum daya daga cikin Hausawa da Fulani.
Alhaji Ya’u PJ wanda ya bayyana haka a tattaunawarsa da wakilinmu ya ce wadanda aka nada shugabannin rikon ba su taba tunanin Jam’iyyar APC za ta ci zabe ba. Don haka dukkansu jam’iyyar ba ta ci mazabunsu ba. Amma da suka ga ta samu nasara, sai suka zo suna cewa wai sun zabi jam’iyyar.
“Ganin rashin adalci da aka yi mana, mun rubuta takardar kuka zuwa ga Mai girma Gwamna muka mika masa da shugaban jam’iyyar na jihar da shugaban jam’iyyar na karamar Hukumar Bassa, amma har yanzu ba mu ji komai ba. Don haka muna rokon Gwamna ya dubi wannan kuka namu da idon basira,” inji shi.
Sai ya yi kira ga al’ummar Hausawa da Fulani na karamar hukuma su kwantar da hankalinsu su ci gaba da bai wa gwamnatin jihar goyon baya da hadin kai.