Gwamnatin Filato da Jami’ar Jos sun yi ta’aziyyar marigayi Bisalla

Gwamnatin Jihar Filato ta aika tawagar jami’anta domin yin ta’aziyya ga iyalan marigayi Malam Abubakar Maina Bisalla mahaifin Mataimakin Editan jaridar Daily Trust Malam Suleiman Bisalla wanda ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata.Wakilan gwamnatin a karkashin jagirancin Sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Shedrack Best ta je garin Gindiri da ke karamar Hukumar Mangu domin […]

Gwamnatin Filato da Jami’ar Jos sun yi ta’aziyyar marigayi Bisalla
Gwamnatin Filato da Jami’ar Jos sun yi ta’aziyyar marigayi Bisalla

Gwamnatin Jihar Filato ta aika tawagar jami’anta domin yin ta’aziyya ga iyalan marigayi Malam Abubakar Maina Bisalla mahaifin Mataimakin Editan jaridar Daily Trust Malam Suleiman Bisalla wanda ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata.
Wakilan gwamnatin a karkashin jagirancin Sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Shedrack Best ta je garin Gindiri da ke karamar Hukumar Mangu domin yin ta’aziyya ga iyalan marigayin.
Lokacin da yake mika sakon ta’aziyyar Farfesa Best ya yaba gudunmawar da marigayin ya bayar tare da kira ga ’ya’yansa su yi koyi da shi domin ci gaban al’ummarsu da Jihar Filato da Najeriya baki daya.
Sauran wadanda suka ziyarci iyalan domin yi musu ta’aziyya sun hada da tsohon Shugaban Hukumar kidaya ta kasa Cif Sumu’ila Danko Makama da Shugaban Jami’ar Jos Farfesa Heyward Mafuyai da tsohon Shugaban Majalisar Dokoki ta Jihar Filato Mista John Clark Dabwan da kuma wakilai daga ofishin Daily Trust na Jos.
Marigayi Abubakar Maina Bisalla, wanda shi ne Sarkin Yamman Gindiri, ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 17 da jikoki 37 da tattaba kunne da dama. Daga cikin ’ya’yansa akwai Malam Suleiman Bisalla da A’ishatu Adamu Daraktar Lafiya ta karamar Hukuma Toto a Jihar Nasarawa da Dije Usman Watse ta Asusun Daidaita Farashin Man Fetur (PEF) da Mohammed Maina Bisalla na Hukumar Kula da Sufuri ta Ruwa ta Najeriya da Hauwa Sani Sa’idu Dawop ta Babbar Kotun Abuja da Rakiya M. Bisalla ta Hukumar Ilimi ta Birnin Tarayya da sauransu. An yi jana’izarsa a ranar Juma’ar da ya rasu kamar yadda addinin Musulunci ya nuna.