Gwamnatin Filato ta daina biya wa jama’a kujerun Hajji da Jerusalem
Gwamnatin Jihar Filato ta dakatar da daukar nauyin biyan kudin kujerun aikin Hajji da na masu ziyara zuwa Jerusalem da take yi a kowace shekara. Gwamnan Jihar Barista Simon Bako Lalong ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa al’ummar jihar jawabi a kan cika shekara daya da hawa kujerar Gwamnan Jihar, inda […]
Gwamnatin Jihar Filato ta dakatar da daukar nauyin biyan kudin kujerun aikin Hajji da na masu ziyara zuwa Jerusalem da take yi a kowace shekara.
Gwamnan Jihar Barista Simon Bako Lalong ne ya bayyana haka a lokacin da yake yi wa al’ummar jihar jawabi a kan cika shekara daya da hawa kujerar Gwamnan Jihar, inda ya ce har wa yau gwamnatin ta dakatar da bayar da kudin da take yi, a lokutan bukukuwan Kirsimeti da azumi da Sallah domin sayen kayayyakin da ake raba wa jama’a. Ya ce gwamnatin ta dauki wadannan matakai ne saboda halin rashin kudin da ake fama da shi a jihar da kasa baki daya.
Gwamnan ya kuma ce a shekara daya da gwamnatinsa ta yi ta samu nasarar dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali ta hanyar sasanta al’ummar jihar.
Ya ce duk da irin dimbin bashin kudi da gwamnatinsa ta gada sama da Naira biliyan 222 daga tsohuwar gwamnatin jihar, gwamnatinsa ta samu nasarar kammala wasu ayyukan hanyoyin mota da yin wasu sababbin hanyoyi a jihar.
Har ila yau, ya ce sun samu nasarar rage yawan bashin albashin da ma’aikatan jihar suke bi. Kuma ya ce gwamnatin jihar ta samu nasarar kwato Naira biliyan biyu da miliyan 700 da aka sace a Hukumar Ilimi Bai-daya ta Jihar (SUBEB).
Ya ce tuni gwamnatin jihar ta rubuta wa Hukumar EFCC wasika kan wadanda ake zargi da sace kudaden jihar don ta zo ta bincika.