Gwamnatin Filato ta dauki nauyin alhazai 398 a bana
Gwamnatin Jihar Filato ta ce duk da mawuyacin halin da tattalin arziki da ake ciki a kasar nan, ta daukin nauyin alhazai 398 don gudanar da aikin Hajjin bana. Shugaban Kwamitin Gudanar da Aikin Hajjin bana na Jihar Filato Alhaji danlami Abdullahi Muhammad ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen taron […]
Gwamnatin Jihar Filato ta ce duk da mawuyacin halin da tattalin arziki da ake ciki a kasar nan, ta daukin nauyin alhazai 398 don gudanar da aikin Hajjin bana.
Shugaban Kwamitin Gudanar da Aikin Hajjin bana na Jihar Filato Alhaji danlami Abdullahi Muhammad ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wajen taron ban-kwana da maniyyatan jihar da aka gudanar a ranar Talatar da ta gabata a garin Jos.
Alhaji danlami ya ce kananan hukumomin jihar sun dauki nauyin maniyyata 150.
Ya ce a bana alhazai 1,273 ne za su tafi aikin Hajjin bana.
Kuma ya ce a karon farko gwamnatin jihar za ta dauki raba wa alhazan jihar abinci kyauta a Mina da filin Arafa a lokacin aikin Hajjin.
Kazalika ya ce gwamnatin jihar ta sayo motocin bas-bas guda biyar masu daukar mutum 45 don jigilar maniyyata daga filin jirgin saman Jiddah.
Sai ya yi kira ga alhazan su kasance masu bin doka da oda a lokacin aikin Hajjin bana, don kare mutuncin Najeriya.
A jawabin Gwamnan Jihar Filato Simon Lalong ya bukaci maniyyatan jihar su zamanto jakadu nagari a lokacin aikin Hajjin.
Gwamnan wanda Mataimakinsa Farfesa Sonni Gwanle Tyoden ya wakilta ya ce a kowace shekara ana yaba wa alhazan jihar wajen nuna halaye nagari a lokacin aikin Hajji. “Don haka ina rokon ku ci gaba da nuna irin wadannan halaye don kare mutuncin jihar nan da kasar nan baki daya,” inji shi.
Kuma ya yi kira ga maniyyatan kan su yi wa Jihar Filato da kasar nan baki daya addu’o’in alheri a lokacin aikin Hajjin.