Gwamnatin Filato ta dauki nauyin Musulmi 400 a aikin Hajjin bana
Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang ya ce gwamnati da kananan hukumomin jihar sun dauki nauyin biya wa Alhazai 400 kudin kujerun aikin Hajjin bana. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabin ban- kwana ga alhazan jihar a ranar Lahadin da ta gabata a garin Jos.Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta tallafa wajen […]

Gwamnan Jihar Filato Jonah Jang ya ce gwamnati da kananan hukumomin jihar sun dauki nauyin biya wa Alhazai 400 kudin kujerun aikin Hajjin bana. Gwamnan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabin ban- kwana ga alhazan jihar a ranar Lahadin da ta gabata a garin Jos.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta tallafa wajen ganin an samar wa alhazan jihar masaukai masu inganci a biranen Madina da Makka don su gudanar aikin hajjin a cikin jin dadi.
Gwamnan wanda Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Jihar Alhaji Ibrahim Idi Waziri ya wakilta ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta cigaba da ba al’ummar jihar damar gudanar da addininsu ba tare da nuna bambanci ba.
Ya yi kira ga alhazan su zamanto jakadu nagari ga jihar da Najeriya a lokacin da suke gudanar da aikin Hajji a kasa Mai tsarki. Kuma ya yi kira ga alhazan su yi addu’o’in samun zaman lafiya da hadin kai ga Najeriya.
A jawabin Amirul Hajji na Jihar na bana Mai martaba Sarkin Kanam Alhaji Babangida Muhammad Mu’azu ya ce Hukumar Alhazan ta Jihar ta kammala shirye-shiryen aikin Hajjin tun daga nan gida zuwa kasa Mai tsarki.
Ya yi kira ga Alhazan su zamanto masu halaye nagari tare da kiyaye dokokin kasar Saudiyya.
Tun farko a jawabin Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Alhaji Salisu Musa ya ce maniyyata 1,300 ne za su tafi aikin Hajji a bana daga jihar. Ya ce daga cikinsu mutum 900 ne suka biya kudin kujerunsu, a yayin da gwamnatin jihar da kananan hukumominta suka dauki nauyin biyan kudin kujera 400. Ya ce an riga an kammala shirya duk takardu da kudin guzurin Alhazan.