Gwamnatin Filato ta himmatu wajen sasanta Fulani da Berom
Gwamnatin Jihar Filato ta himmatu wajen sasanta Fulani da Berom don kawo karshen rikicin kabilanci da ke gudana a tsakaninsu. Gwamnan Jihar Barista Simon Lalong ne ya bayyana haka a yayin zaman da ya yi da shugabannin Fulani da Berom da suka fito daga karamar Hukumar Riyom da Barikin Ladi inda ya sanar da kafa […]
Gwamnatin Jihar Filato ta himmatu wajen sasanta Fulani da Berom don kawo karshen rikicin kabilanci da ke gudana a tsakaninsu. Gwamnan Jihar Barista Simon Lalong ne ya bayyana haka a yayin zaman da ya yi da shugabannin Fulani da Berom da suka fito daga karamar Hukumar Riyom da Barikin Ladi inda ya sanar da kafa kwamitin da zai kawo karshen hare-haren da kabilun biyu suke kai wa juna.
Gwamna Lalong ya ce ya shirya wannan zama ne don ya ba shugabannin kabilun damar amayar da duk abin da ke ci musu tuwo a kwarya daga nan sai a tattauna yadda za a gano bakin zaren rikicin.
A yayin zaman na ranar Alhamis Gwamnan ya ce ya gana da shugabannin kabilun a lokuta mabambanta ne don ya bi diddigin musabbabin rikicin, inda abin ya ba kowane bangare damar ya bayyana korafe-korafensa. “Na yanke hukuncin in tattauna da su ne don ganin yadda za a kawo karshen wannan rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa. Daga farko na tattauna jami’an tsaro, daga nan na zauna da Fulani, suka bayyana korafe-korafensu, daga baya na zauna da Berom, abin da na fahimta a lokacin tattaunawar, dukkan bangarorin sun gaji da rikicin, burinsu a samu zaman lafiya mai dorewa,” inji shi.
Lalong ya ce burin kowace gwamnati shi ne a samu zaman lafiya, haka ne dalilin ganawar da ya rika shiryawa cikin wata biyu da suka gabata don a samu zaman lafiya.
Kwamishinan ’Yan sandar Jihar Filato Nasiru Oki a lokacin da yake tattaunawa da ’yan jarida bayan nada kwamitin, ya ce tattaunawar za ta haifar da da mai ido wajen kawo karshen rikici a tsakanin kabilun biyu.
Oki ya ce an kafa kwamitin ne, aka dora masa alhakin duba wasu hanyoyin da zai tattauna da shugabannin kabilun don samar da zaman lafiya mai dorewa.
Alhaji Idris Gidado Dagacin Gashish wanda ya wakilci Fulani ya ce wannan ne lokaci na farko da gwamnati ta zauna da bangarorin biyu don neman maslaha a kan rikicin.
Alhaji Gidado ya yaba wa Gwamna Lalong kan jajircewar da yake yi wajen ganin an samu zaman lafiya mai dorewa, ya ce yana da karfin gwiwar za a samu zaman lafiya mai dorewa a tsakanin bangarorin biyu.
Mista Pam Gyang wanda ya wakilci Berom ya ce a shirye ’yan kabilarsa suke wajen ganin an samu zaman lafiya kamar yadda iyaye da kakanninsu suka zauna da Fulani.
Gyang ya ce Fulani da Berom suna zaune lafiya, suna magana da harshe daya, sannan akwai auratayya tsakaninsu, amma abin bakin ciki wannan rikici na neman wadannan abubuwa su zama tarihi. Ya ce sakamakon tattaunawar da aka yi manoma za su je gonakinu, sannan Fulani za su yi kiwo ba tare da tunanin tashin hankali ba.