Gwamnatin Filato ta kaddamar da aikin gyara hanyoyin cikin garin Jos
Gwamnatin Jihar Filato ta kaddamar da aikin gyara hanyoyi 28 da ke cikin garin Jos babban birnin Jihar Filato. An kaddamar da aikin gyara hanyoyin ne, a hanyar da ta tashi daga mararrabar Zololo zuwa Nasarawa Gwom da ’Yan shanu da Rikkos da ke cikin garin Jos.Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Filato Mista Sunday […]
Gwamnatin Jihar Filato ta kaddamar da aikin gyara hanyoyi 28 da ke cikin garin Jos babban birnin Jihar Filato.
An kaddamar da aikin gyara hanyoyin ne, a hanyar da ta tashi daga mararrabar Zololo zuwa Nasarawa Gwom da ’Yan shanu da Rikkos da ke cikin garin Jos.
Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka ta Jihar Filato Mista Sunday Gyang da Mataimakin Shugaban Ma’aikata na Gidan Gwamnatin Jihar Barista Yusuf Gambo Hawaja da wasu jami’an gwamnatin jihar ne suka halarci wajen kaddamar da aikin.
Da yake zantawa da ’yan jarida a wurin kaddamar da aikin, Barista Yusuf Gambo Hawaja ya ce wannan aiki ya kunshi gyara hanyoyin da ke cikin garin Jos ne ba gina sababbi ba. Ya ce idan aka lura hanyoyin cikin garin Jos da kewaye duk sun lalace kuma tun a lokacin da Gwamnan Jihar Simon Lalong yake yakin neman zabe ya yi alkawarin gyara hanyoyin, ganin yadda lalacewar hanyoyin ta yi kamari, don haka a yanzu ya ba da umarnin a yi gaggawar gyara su.
Ya ce nan gaba duk hanyoyin da suka dace a yi sababbi, za a yi sababbin a wuraren, sai ya yi kira ga al’ummar garin Jos su zauna lafiya da junansu kuma su ci gaba da bai wa gwamnatin jihar goyon baya da hadin kai.