Gwamnatin Filato ta kafa dokar hana yin bara a jihar 1
Gwamnatin Jihar Filato ta bi sahun wasu jihohi da suka hana barace-barace inda ta kafa dokar hana yin yin bara a jihar.Da yake zantawa da ’yan jarida kan dokar ta hana yin bara da aka kafa a jihar, Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Filato Mista AbrahamcYiljap ya ce gwamnatin jihar ta fahimci cewa nakasassu sun […]

Gwamnatin Jihar Filato ta bi sahun wasu jihohi da suka hana barace-barace inda ta kafa dokar hana yin yin bara a jihar.
Da yake zantawa da ’yan jarida kan dokar ta hana yin bara da aka kafa a jihar, Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Filato Mista AbrahamcYiljap ya ce gwamnatin jihar ta fahimci cewa nakasassu sun mamaye manyan titunan jihar musamman garin Jos.
Ya ce kuma akwai nakasassu da aka kawo su daga wasu wurare da ba su sani ba, kuma mutanen da suka kawo irin wadannan nakasassu suna tallarsu a wurin masu wucewa, inda ya ce hakan bai kamata ba.
Har ila yau ya ce “game da tsaro mun samu zaman lafiya a Jihar Filato kuma muna son wannan zaman lafiya ya dore. Saboda haka duk wadanda suke tafiya suna bara a kan tituna a Jihar Filato ba mu san manufarsu ba. Don haka gwamnatin jihar ta kafa wannan doka ta hana yin bara a jihar.”
Ya ce gwamnatin Jihar Filato ba ita ce ta fara kafa dokar hana yin bara ba, inda ya ce zuwa yanzu akwai jihohin Arewa da dama da suka kafa irin wannan doka.
Kwamishina Yiljap ya ce akwai wuraren da aka ware don tallafa wa nakasasu a jihar kamar Ma’aikatar Harkokin Mata da Ma’aikatar Kiwon Lafiya da sauran kungiyoyin da suke tallafa wa nakasasu. Don haka ya yi kira ga nakasasun su tuntubi irin wadannan wurare.
Ya ce gwamnatin jihar tana son jama’a su fahimci cewa ba an kirkiro wannan doka ce don a kuntata wa wani ba. Don haka ya yi kira ga jama’ar jihar kan su ba da goyon baya da hadin kai kan wannan doka da aka kafa.
Da yake zantawa da wakilinmu kan dokar hana yin bara a Jihar Filato, Sarkin Kutaren Jos Alhaji Ibrahim Nuhu ya ce matukar gwamnatin Jihar Filato za ta zauna da su ta tallafa musu za su ba ta goyon baya da hadin kai kan wannan doka ta hana yin bara da aka kafa.
Ya ce “Muna da yara kanana da muke bukatar gwamnatin Jihar Filato ta dauki nauyin karatunsu kuma muna bukatar a koya mana sana’o’i a ba mu jari, idan gwamnatin ta yi mana wadannan abubuwa a shirye muke mu ba da goyon baya da hadin kai kan wannan doka da aka kafa.”