Gwamnatin Filato ta kara sassauta dokar hana fita a Jos
Daga yanzu dokar ta tashi daga qarfe 7 na safe zuwa karfe 3 na yamma, ta koma karfe 6 na safe zuwa karfe 6 na yamma.
Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang
Gwamnatin Jihar Filato ta kara sassauta dokar hana fita, a garin Jos.
Daga yanzu dokar ta tashi daga karfe 7 na safe zuwa karfe 3 na yamma, ta koma karfe 6 na safe zuwa karfe 6 na yamma.
Wata sanarwa wadda ke dauke da sanya hanun Kwamishinar Watsa Labarai da Sadarwa ta jihar, Joyce Lohya Ramnap ta ce an sassauta dokar ne ganin yadda zaman lafiya da kwanciyar hankali ya fara samuwa, a Karamar hukumar Jos ta Arewa.
Wani mummunan hari da aka kashe mutum akalla 27 a Unguwar Rukuba, a makon da ya gabata, ya sanya gwamnati ta sanya dokar hana fita, bayan da ta tattauna da jami’an tsaro.
Sanarwar ta ce wannan sassauta dokar, za ta fara aiki ne daga ranar Larabar nan.
- Gwamnatin Filato ta kara sassauta dokar hana fita a Jos
- Shinkafa da taliya ba za su sa ka ci zaɓen 2027 ba —Atiku ga Tinubu
Ta bukaci mazauna garin, su cigaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum tare da kasancewa masu bin doka da oda, a cikin sa’o’in da aka sassauta dokar.
Ta ce gwamnan jihar, Barista Caleb Mutfwang ya umarci jami’an tsaro, su tabbatar sun ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, a dukkan wuraren da wannan al’amari ya shafa.