Gwamnatin Filato ta nuna farin ciki da samun zaman lafiya a jihar

Mai ba Gwamnan Jihar Filato shawara kan harkokin tsaro, Barista Timothy Baba Parlong ya ce gwamnatin jihar tana matukar farin ciki da samun zaman lafiya da aka fara a jihar. Barista Timothy Parlong ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin taron zaman lafiya tare da kaddamar da ’yan banga da al’ummar […]

Gwamnatin Filato ta nuna farin ciki da samun zaman lafiya a jihar

Mai ba Gwamnan Jihar Filato shawara kan harkokin tsaro, Barista Timothy Baba Parlong ya ce gwamnatin jihar tana matukar farin ciki da samun zaman lafiya da aka fara a jihar.
Barista Timothy Parlong ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wurin taron zaman lafiya tare da kaddamar da ’yan banga da al’ummar mazabar Abba Na-Shehu da ke garin Jos suka shirya.
Ya ce tabbatar da zaman lafiya nauyi ne da kan gwamnati, saboda haka zaman lafiyar da aka fara samu a Jihar Filato babban abin farin ciki ne ga gwamnatin jihar, musamman ganin irin kokarin da ta yi na ganin
an samu zaman lafiya a jihar.
Ya ce a lokacin da aka samu rikice-rikice a jihar, gwamnati ta hada kai da kungiyoyi masu zaman kansu da suke fafutikar neman zaman lafiya, inda aka rika bi ana wayar da kan jama’a kan muhimmancin zaman lafiya.
Barista Parlong ya ce a yanzu al’ummar jihar nan fahimci muhimmancin zaman tare, don haka babu wanda zai rude su ya sa a sake tayar da wani rikici a jihar.
Ya yabawa wadanda suka shirya taron musamman ganin hanyar Bauchi Road da ta ratsa garin Jos da wasu suke tsoron bi a da, tana cikin wannan unguwa kuma a yanzu kowa yana bin hanyar ba tare da tsoro ba.  Ya ce babu shakka wannan ya nuna cewa lallai an samu zaman lafiya a garin Jos.
Ya yi kira ga jama’ar jihar su ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da aka fara samu, domin suna ganin yadda kowa yake gudanar da harkokinsa a cikin cikin jin dadi da kwanciyar hankali sakamakon zaman lafiyar da aka samu a jihar. Daga nan sai ya yi alkawarin dinka yunifom ga ’yan bangar da aka kafa a unguwar.
A jawabin daya daga cikin dattawan garin Jos kuma Matawellen Toro, Alhaji Baban Iya Muhammad ya ce sun shirya taron ne saboda ganin zaman lafiyar da aka fara samu a garin Jos.
Matawallen ya ce  amma a halin yanzu muna fama da matsalar yaranmu na cikin garin Jos, inda wasu suka zama ’yan sara-suka da kwace wa mata wayoyin hannu da sace-sacen kananan yara da sauran miyagun abubuwa.
Ya ce saboda haka ne suka ce babu abin da ya kamata su yi kan wannan al’amari sai su kafa  yaranmu masu kishi a matsayin ’yan banga domin su ba da gudunmawarsu su hada kai da sojoji da ’yan sanda don ganin an magance wadannan matsaloli.
Ya ce muna son wadannan yara ’yan banga da muka kafa su shiga dukkan lungun da ake aikata irin wadannan miyagun ayyuka a cikin gari domin su hana. Ya yi kira ga iyayen yara da ke Jos kan kowa ya ja wa ’ya’yansa kunne domin a ci gaba da dorewar zaman lafiyar da aka samu a garin.