Gwamnatin Filato ta sake dawo da dokar hana fita

Saboda haka Gwamnatin jihar a yanzu ta sake dawo da dokar hana fitar ta sa’o’i 24.

Gwamnatin Filato ta sake dawo da dokar hana fita

Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong

Wasu matasa sun fasa runbunan da aka ajiye kayayyakin abinci na tallafin COVID-19 da gwamnatin tarayya ta aikowa jihar Filato, don rabawa al’ummar jihar, suka wawushe kayayyakin a yau Asabar din nan.

Sakamakon haka ya sanya Gwamnatin jihar Filato ta sake dawo da dokar hana fita ta sa’o’i 24 da ta kafa, a ranar Talatar da ta gabata, bayan da ta sassauta dokar daga karfe 6 na safe zuwa 8 na dare, a jiya juma’a.

Wata sanarwa da gwamnan jihar Simon Lalong ya fitar ce ta bayyana haka.

Sanarwar ta ci gaba da cewa “an shimfida dokar takaita zirga-zirgar ne ganin abinda wasu bata gari suka yi a yau Asabar, na fasa rumbunan da aka ajiye kayayyakin abinci na tallafin annobar Covid-19 da gwamnatin tarayya ta aikowa jihar, da kuma ganin yadda wannan mummunan lamari yake neman ya ci gaba, ta yadda zai iya zama barazana ga zaman lafiya a jihar.”

“Saboda haka Gwamnatin jihar ta sake dawo da dokar hana fitar ta sa’o’i 24, a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu.”

“Gwamnatin jihar ta yi hakan ne domin tabbatar da tsaro da kare dukiyoyin al’umma wanda yanzu suke cikin barazana.”