Gwamnatin Filato ta sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24
Gwamnatin ta sassauta dokar ne biyo bayan daidaitar al’amura a yankin.
Gwamnatin Jihar Filato, ta sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 a yankin Jos-Bukuru, biyo bayan rikiɗewar zanga-zangar matsin rayuwa zuwa tarzoma.
Yanzu mutane a yankin za su iya zirga-zirga daga ƙarfe 7 na safe zuwa 7 ƙarfe na yamma, wanda matakin zai fara aiki daga ranar Talata.
Dokar hana fita ta fara ne a ranar 4 ga watan Agusta bayan da zanga-zangar “EndBadGovernance” ta koma tashin hankali a Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa.
Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa an samu zaman lafiya, wanda hakan ya sa aka sassauta dokar hana fita.
Gwamnan jihar, Caleb Mutfwang da hukumomin tsaro a jihar, sun amince domin sassauta dokar da nufin bai wa jama’a damar ci gaba da al’amuransu na yau da kullum.
Gwamnatin za ta ci gaba da nazarin game da halin da ake ciki a yankin.
Gwamnan, ya kuma yi kira ga mazauna yankin Jos-Bukuru su haɗa kai da jami’an tsaro tare da bayar da rahoton duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya.