Gwamnatin Filato za ta binciki rushewar ginin Islamiyyar da ya hallaka yara 6 a bukur
Gwamnatin Jihar Filato za ta kafa kwamitin da zai binciki musababbin rushewar ginin wata makarantar Islamiyya mai suna Abu Ni’iman Pribate School a garin bukur da ke karamar Hukumar Jos ta Kudu, inda ya yi sanadin rasuwar dalibai 6 tare da raunata 25 a yammacin Lahadin da ta gabata. Gwamnan Jihar, Barista Simon Lalong ne […]
Gwamnatin Jihar Filato za ta kafa kwamitin da zai binciki musababbin rushewar ginin wata makarantar Islamiyya mai suna Abu Ni’iman Pribate School a garin bukur da ke karamar Hukumar Jos ta Kudu, inda ya yi sanadin rasuwar dalibai 6 tare da raunata 25 a yammacin Lahadin da ta gabata.
Gwamnan Jihar, Barista Simon Lalong ne ya bayyana haka a lokacin ya kai ziyarar jaje ga iyayen yaran da hadarin ya rutsa da su, inda ya ce gwamnatin jihar za ta binciki lamarin ne domin ganin an dauki matakan kare sake faruwar irin hakan a nan gaba, don kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar.
Gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta dauki nauyin biyan kudin jinyar wadanda suka ji rauni a hadarin.
Da yake zantawa da wakilinmu, daya daga cikin iyayen daliban da suka rasu mai suna Yusuf Garba da ya ce dansa Abubakar Yusuf ya rasu a hadarin, ya ce “Ba na gida sai mahaifiyarsa ta kira ni a waya, ta ce in yi maza in zo ginin makarantar ya rushe da danmu.”
Ya ce da ya zo sun yi ta kokari su ciro yaran da hadarin ya rutsa da su a karshe suka gano dansa na cikin wadanda suka rasu a hadarin.
Ya ce yara shidan da suka rasu an yi jana’izarsu a ranar Litinin, kuma yara 25 ne suka ji rauni a hadarin.
Daraktar kungiyar Mata Musulmi ta garin bukur kuma Sakatariyar kungiyar Mata Musulmi (FOMWAN) reshen Jihar Filato, Hajiya Binta Hassan Hussaini ta bayyana wa wakilinmu cewa, tana zaune a gida da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Lahadi, sai aka zo aka ce mata ginin makarantar ya rushe. “Da muka je wurin sai na ga jama’a sun taru abin tausayi kowa yana kokarin ya ceci rayukan yaran. A lokaci ma’aikatan kwana-kwana da jami’an Hukumar Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) sun zo wajen don aikin ceto yaran. Kuma wannan abu ya faru ne bayan daukewar ruwan saman da aka yi a garin,
lokacin da yara suke karatu,” inji ta.
Ta yi kira ga gwamnati kan ta rika sanya ido a kan dukkan gine-ginen da ake yi a kasar nan, domin kauce wa faruwar irin wadannan abubuwa.
Daraktar ta ce su ma jama’a ya kamata su rika lura da irin wannan al’amari suna magance su, ba sai abu ya faru ba, a zo ana cewa da an yi kaza da irin haka ba ta faru ba.
Ko’odinetan Hukumar NEMA a Shiyyar Arewa ta Tsakiya Alhaji Muhammad Abdulsalam ya ce a lokacin da al’amarin ya faru, nan take jami’an hukumar suka isa wurin. Ya ce yaran da hadari ya rutsa da su ’yan kimanin shekara 8 ne zuwa 13 ne.
“Mun fito da gawarwakin yara 6, daga cikin ginin da ya rushe, hudu mata biyu maza da yara 24 da suka samu raunuka. Mun kwashi yara 5 da suka samu munanan raunuka zuwa Asibitin kwararru na Jihar Filato, yayin da aka sallami yaran da raunukansu ba masu muni ba ne, bayan da aka yi masu magani a wasu kananan asibitoci da ke bukur,” inji shi.
Wakilinmu ya yi kokarin ganawa da shugabannin makarantar, don jin ta bakinsu kan al’amarin, amma abin ya ci tura domin an ce ba sa nan.