Gwamnatin Filato za ta dauki malaman firamare 4000
Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Filato Malam Muhammad Nazifi ya bayyana cewa zuwa yanzu gwamnatin jihar ta kammala duk shirye-shirye domin daukar malaman makarantun firamare don rarraba su a makarantun firamaren jihar. Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron ’yan jarida na wata-wata da kwamishinonin jihar suka fara gudanarwa […]
Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Filato Malam Muhammad Nazifi ya bayyana cewa zuwa yanzu gwamnatin jihar ta kammala duk shirye-shirye domin daukar malaman makarantun firamare don rarraba su a makarantun firamaren jihar.
Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron ’yan jarida na wata-wata da kwamishinonin jihar suka fara gudanarwa a garin Jos, inda ya ce nan ba da dadewa ba za a raba wa malaman da aka dauka takardun daukarsu aiki.
Ya ce a kokarin gwamnatin jihar na sake farfado da harkokin kasuwanci a jihar, ta kulla yarjejeniya da wani kamfani da ke kasar Ingila mai suna Rougton International Energy Associates Consortium don sake gina babbar kasuwar Jos da ta kone shekara 12 da suka gabata.
Haka zalika ya ce gwamnatin jihar ta samu nasarar biyan albashin da ma’aikatan jihar suke bi tun daga watan Yulin bara zuwa watan Mayun bana.
Haka kuma ya ce gwamnatin jihar ta samu nasarar kammala ayyukan hanyoyin mota daga Jos zuwa Maza da Mangu da Gindiri zuwa Lere da Dogon karfe zuwa Tudun Wada zuwa Unguwan Yashi da Zololo zuwa Nasarawan Gwom.