Gwamnatin Filato za ta farfado da kamfanin buga jaridun jihar
Gwamnatin Jihar Filato za ta farfado da kamfanin dab’i na jihar (PPP) wanda ke buga jaridun Standard da ya yi shekara da shekaru a some. Kwamishinan Watsa Labarai da Sadarwa na Jihar, Malam Nazifi Ahmed ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga ma’aikatan kamfanin a garin Jos, a ci gaba da ziyarar […]

Gwamnatin Jihar Filato za ta farfado da kamfanin dab’i na jihar (PPP) wanda ke buga jaridun Standard da ya yi shekara da shekaru a some.
Kwamishinan Watsa Labarai da Sadarwa na Jihar, Malam Nazifi Ahmed ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga ma’aikatan kamfanin a garin Jos, a ci gaba da ziyarar da yake yi zuwa sassan da suke karkashin ma’aikatarsa.
Kwamishinan ya ce abin bakin ciki a ce gwamnati tana da irin wannan kamfani da ke kunshe injinan da za su iya buga kowace jarida ko littafi ko takarda tare da kwararrun ma’aikata, amma a yi watsi da shi ba a yin komai.
Malam Nazifi ya ce gwamnatocin da suka gabata sun yi watsi da kamfanin, domin ko gwamnatin da ta gabata ta kashe sama da Naira miliyan 260 wajen sayo sababbin injina na zamani, amma aka yi watsi da injinan shekara biyu ba tare da kafa su ba.
Kwamishinan ya ce in Allah Ya yarda wannan gwamnati za ta kafa injinan, domin a ci gaba da amfani da su a kamfanin.
Har ila yau ya ce “za mu jawo hankalin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar nan da kananan hukumominta, domin su rika kawo ayyukan buga takardunsu ga kamfanin nan. Yin haka shi ne zai farfado da kamfanin.”
Ya yi kira ga ma’aikatan kamfanin su bai wa gwamnatin mai kudirin ceto al’ummar jihar daga mawuyacin halin da suka shiga a baya, goyon baya ta hanyar zuwa wurin aiki a kan lokaci tare da rike gaskiya da amana a aikinsu.