Gwamnatin Filato za ta gina sabon ofishin hukumar alhazai

Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya ce gwamnati jihar ta kammala shirin gina sabon ofishin hukumar alhazai ta jihar a garin Jos. Gwamna Lalong ya bayyana haka ne lokacin da yake ban-kwana da maniyatan jihar a filin wasa na Rwang Pam da ke garin Jos.Ya ce tuni gwamnatin jihar ta samu wani babban fili […]

Gwamnatin Filato za ta gina sabon ofishin hukumar alhazai
Gwamnatin Filato za ta gina sabon ofishin hukumar alhazai

Gwamnan Jihar Filato Barista Simon Lalong ya ce gwamnati jihar ta kammala shirin gina sabon ofishin hukumar alhazai ta jihar a garin Jos.
Gwamna Lalong ya bayyana haka ne lokacin da yake ban-kwana da maniyatan jihar a filin wasa na Rwang Pam da ke garin Jos.
Ya ce tuni gwamnatin jihar ta samu wani babban fili da za ta gudanar da aikin a cikin garin Jos, kuma ya ce idan aka kammala aikin ginin sabon ofishin alhazan jihar da ma’aikatan hukumar za su samu isassahen wajen da za su rika shirye-shiryen gudanar da aikin Hajji duk shekara a cikin walwala da jin dadi.
Gwamnan wanda Mataimakinsa Farfesa Sonni Tyoden ya wakilta, ya bai wa alhazan jihar da suka biya kudadensu a bara, amma ba su samu tafiya aikin Hajji ba, cewa gwamnatin jihar tana iyakar kokarinta, wajen ganin ta kwato musu kudadensu.
Ya ce tuni gwamnatin jihar ta kai jami’an da ake zargi da cinye kudaden alhazan ga Hukumar EFCC don ganin an kwato musu kudadensu tare da gurfanar da jami’an a gaban kotu.
Ya yi kira ga alhazan jihar na bana, su zamanto jakadu nagari ga jihar kuma su yi wa jihar addu’o’in ci gaba da samun zaman lafiya da Najeriya baki daya.
Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Alhaji Ayuba Salihu Kwande, ya ce a bana cikin kujera 1,239 da Hukumar Hajji ta kasa ta bai wa jihar, kujera  997 ne aka biya a jihar. “A bana alhazan Jihar Filato sun biya Naira miliyan 1 da dubu 35, a kan matsakaiciyar kujerar Hajji da za a bai wa kowane Alhaji guzurin Dala 750.Wannan ya nuna cewa a duk jihohin Arewa ta Tsakiya babu jihar da aka samu saukin kudin kujerar kamar Jihar Filato,” inji shi.
Ya yaba wa gwamnatin jihar kan yadda ta dauki nauyin biyan kudaden kama wa alhazan jihar masauki a kasa Mai tsarki tare da bayar da kudin da aka sayo wa alhazan jihar magungunan da za su yi amfani da su a lokacin aikin Hajjin.
A jawabin Amirul Hajji na Jihar, Mai martaba Sarkin Wase Dokta Muhammad Sambo Haruna ya mika godiyarsa ga Gwamnan kan jagorancin alhazan da aka ba shi. Ya yi kira ga alhazan su dauki aikin Hajjin da matukar mahimmanci kuma su yi addu’o’i ga jihar da Najeriya baki daya.