Gwamnatin Filato za ta kammala aikin hanyar Jos zuwa Bukur
Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Filato Barista Yusuf Gambo Hawaja ya ce gwamnatin jihar, a karkashin Gwamna Simon Lalong za ta kammala aikin hanyar Jos zuwa Bukur tare da sauran hanyoyin da tsohuwar gwamnatin jihar ta faro ba ta kammala ba. Barista Yusuf Gambo Hawaja ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa […]
Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Filato Barista Yusuf Gambo Hawaja ya ce gwamnatin jihar, a karkashin Gwamna Simon Lalong za ta kammala aikin hanyar Jos zuwa Bukur tare da sauran hanyoyin da tsohuwar gwamnatin jihar ta faro ba ta kammala ba.
Barista Yusuf Gambo Hawaja ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce “za mu kammala wadannan hanyoyi kafin mu fara wasu, domin gwamnati ci gaba ne kuma hanyoyin za su kyautata rayuwar al’ummar jihar,” inji shi. Barista Hawaja ya ce muhimman abubuwan da gwamnatin jihar ta sanya a gaba su ne cika alkawuran da suka yi wa jama’ar jihar a lokacin da suke yakin neman zabe.
Ya ce wadannan abubuwa su ne dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da biyan ma’aikatan jihar hakkokinsu da gyara asibitoci da bunkasa harkokin noma da na ilimi da gyara cikin garin Jos da kuma gyara babbar kasuwar Jos.
Ya ce idan suka samu nasarar cika wadannan alkawura za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar. Kuma jihar za ta bunkasa ta dawo da martabar da aka santa da ita a nan Najeriya da duniya baki daya.
Ya yi kira ga al’ummar jihar su zauna lafiya kuma su ci gaba da ba sabuwar gwamnatin jihar goyon baya da hadin kai, domin ta samu nasarar aiwatar da kudirorin da ta sanya a gaba.