Gwamnatin Filato za ta kashe Naira miliyan 40 kan ciyar da masu azumi
Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Filato kuma shugaban kwamitin rabon kayayyakin buda baki da gwamnatin Filato ta kafa, Alhaji Ado Isma’ila Shigi, ya ce Gwamnan Jihar Mista Jonah Jang, ya bayar da Naira miliyan 40, inda aka sayo shinkafa da gero da sukari don raba wa Musulmin jihar a wannan wata na azumi […]
Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Filato kuma shugaban kwamitin rabon kayayyakin buda baki da gwamnatin Filato ta kafa, Alhaji Ado Isma’ila Shigi, ya ce Gwamnan Jihar Mista Jonah Jang, ya bayar da Naira miliyan 40, inda aka sayo shinkafa da gero da sukari don raba wa Musulmin jihar a wannan wata na azumi da muke ciki.
Alhaji Ado Isma’ila Shigi ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu, inda ya ce sun lura a baya idan aka raba irin wadannan kayayyaki ba sa isa zuwa ga wadanda suka kamata, don haka a bana sun canja tsarin da ake bi a da sun fito da sabon tsari don ganin kayayyakin sun isa wuraren da suka kamata su isa.
Ya ce Gwamna Jonah Jang yana ba al’ummar Musulmin jihar hakkokinsu gwargwado, don haka ya yi kira ga al’ummar Musulmin jihar su nuna godiyarsu ga Gwamnan kan irin wannan kokarin da yake yi na kyautata musu ta wajen ba gwamnain jihar goyon baya a kan shirye-shiryenta.