Gwamnatin Filato za ta sanya wutar lantarki a kananan hukumomin kuan Pan da Mikang
Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa da Samar da Wutar Lantarki ta Jihar Filato Alhaji Idi Ibrahim Waziri ya ce gwamnatin jihar ta ba da umarnin a sanya wa kananan hukumomin kuan Pan da Mikang wutar lantarki a bana. Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos, inda ya ce gwamnatin […]
Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa da Samar da Wutar Lantarki ta Jihar Filato Alhaji Idi Ibrahim Waziri ya ce gwamnatin jihar ta ba da umarnin a sanya wa kananan hukumomin kuan Pan da Mikang wutar lantarki a bana. Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ’yan jarida a Jos, inda ya ce gwamnatin ta kuduri aniyar sanya wa kananan hukumomin wutar lantarki ne, ganin cewa su ne kadai kananan hukumomin da ba su wutar lantarki a jihar. Ya ce gwamnatin ta kuma ba da umarnin a sanya wa dukkan kyauyukan da suke kusa wutar lantarkin Ya ce “A bana za mu sanya wuta ga kyauyukan da nisansu bai wuce kilomita daya ba da inda wutar take. Ya ce a yankin Wase akwai kauyukan Yola Wakat da Lamba da wasu kauyukan yankin Kanam da muka shirya sanya musu wutar lantarki.” Alhaji Idi Waziri ya ce a bangaren ruwan sha akwai wurare da dama da gwamnatin za ta gyara injunan ba da ruwan sha da suka hada da Bokkos da Langtang da Shendam da Panshing, sai wurare da dama da za a tona musu madatsun ruwa a bana. Sai ya ce gwamnatin ta kashe sama da Naira biliyan 8 don samar da ruwan sha ga mutanen Bukur da Jos inda kamfanonin da suke gudanar da aikin suke ci gaba da gudanarwa. Ya ce a wannan aiki za a gina matatun ruwa uku da za su ba mutanen Unguwar Rimi da Unguwar Rogo da Jami’ar Jos da Unguwar Rukuba wadataccen ruwan sha.