Gwamnatin Filato za ta taimaka wa makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu
Gwamnan Jihar Filato Barisat Simon Bako Lalong ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za tallafa wa makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu da ke jihar domin karfafa musu gwiwa wajen horar da nagartattun jami’an kiwon lafiya. Gwamnan Simon Lalong ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bude makarantar kiwon lafiya […]
Gwamnan Jihar Filato Barisat Simon Bako Lalong ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar za tallafa wa makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu da ke jihar domin karfafa musu gwiwa wajen horar da nagartattun jami’an kiwon lafiya.
Gwamnan Simon Lalong ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wajen bude makarantar kiwon lafiya ta Sahlan a garin Jos, inda ya ce gwamnatin jihar za ta tallafawa irin wadannan makarantu ne, ganin irin taimaka wa gwamnatin jihar da suke yi wajen sauke nauyin da ke kanta wajen kiwon lafiyar jama’a.
Gwamnan ya ce sai dai gwamnatin jihar ba za ta amince a rika yaye daliban da ba su cancanta ba a irin wadannan makarantu, don haka ya umarci Ma’aikatar Lafiya ta Jihar, ta sanya ido wajen ganin ana bin ka’idoji a makarantun.
Gwamna Lalong wanda Mataimakin Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar, Barista Yusuf Gambo Hawaja ya wakilta, ya ce asibitocin da ke jihar, ba za su iya gudanar da ayyukansu ba idan babu irin wadannan makarantu. Don haka ya yi kira ga jami’an makarantun su yi kokarin horar da ma’aikatan kiwon lafiya nagari da za su taimaka wa al’umma wajen kiwon lafiya.
A jawabin Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya ce duk wanda ya yi karatun kiwon lafiya zai taimaki al’umma, musamman mata da suka karanci kiwon lafiyar. Don haka ya yi matukar farin ciki da bude makarantar, wadda ya ce ta zo a daidai lokacin da ake bukatarta.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar ta taimaka wa makarantar ta hanyar daukar nauyin biyan albashin wasu daga cikin malamanta, domin za ta taimaka wa gwamnatin jihar kan harkokin kiwon lafiya.
Sheikh Sani Yahya Jingir wanda Mataimakinsa na Biyu, Sheikh Sa’idu Hassan Jingir ya wakilta, ya yi kira ga daliban makarantar su tsaya su yi karatu tsakani da Allah domin su zo su taimaki al’umma, su kuma malaman makarantar su zamanto babu sani babu sabo a tsakaninsu da kowane dalibin makarantar kan harkokin karatu, domin fannin ya shafi lafiya da rayuwar al’umma ne baki daya.
Tun farko a jawabin Daraktan Makarantar, Malam Muhammad Shafi’u Yakubu ya ce sun kafa
makarantar ce da hadin gwiwar shugaban kamfanin mai na A.A. Rano, Alhaji Auwal Abdullahi, domin su samar da wata babbar cibiya da za ta bayar da gudunmawa kan harkokin kiwon lafiya a Najeriya da duniya baki daya. Ya ce a kokarinsu na cimma wannan manufa, sun yi bincike tare da neman shawarwarin kwararru kan harkokin kiwon lafiya game da dukkan abubuwan da ake bukata a makarantar.