Gwamnatin Gombe ta ɗauki matakan magance matsalar bahaya a fili

Hukumar ta ƙudiri aniyar yaƙi da yin bahaya a fili a jihar.

Gwamnatin Gombe ta ɗauki matakan magance matsalar bahaya a fili

Hukumar Tsaftace Muhalli ta Jihar Gombe (GOSEPA), ta fara ɗaukar ƙwararan matakai don kawar da yin bahaya a fili don inganta tsaftar muhalli a faɗin jihar.

A ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gudanarwa, Dokta Auwalu Baba Jada, hukumar ta mayar da hankali kan gina bayan gida a makarantu, asibitoci, kasuwanni, da tashoshin mota.

Wannan matakin na nufin daƙile ɗabi’ar yin bahaya a fili tare da inganta lafiya da tsaftar muhalli.

A shekarar da ta gabata, GOSEPA ta samu nasarori kamar gyaran magudanun ruwa, sarrafa shara, da samar da wuraren tara shara a jihar.

Sai dai Dokta Baba Jada, ya ce kawar da yin bahaya a fili ita ce babbar manufar hukumar a 2025.

“Idan aka kawar da wannan ɗabi’a, za a samar da al’umma mai lafiya da jin daɗi. Saboda haka, muna gina wuraren yin bahaya don taimaka wa jama’a su daina yi a fili,” in ji shi.

Ya yi kira ga jama’ar Gombe da su tallafa wa ayyukan hukumar tare da mara wa gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, baya wajen inganta tsafta mai ɗorewa a jihar.

A wata sanarwa da mai kula da Sashen Bayanai na hukumar, Abubakar Mohammed Tukur, ya fitar, ya bayyana cewa tawagogin hukumar sun fara ziyartar jama’a don wayar musu da kai game da muhimmancin tsaftar muhalli da bin dokokin tsafta.

Sanarwar ta ce waɗannan matakan na da nufin dacewa da manufofin ƙasa da duniya wajen kawar da yin bahaya a fili.

GOSEPA ta sha alwashin tabbatar da tsaftar jihar nan a shekarar 2025.

An kori jami’an EFCC 27 daga aiki da saboda almundahana

Gwamnan Bauchi ya sallami Kwamishinoninsa

An ceto mutum 36 da aka yi garkuwa da su a Sakkwato

NAJERIYA A YAU: Amfanin Komawa Makaranta A Ranar Da Aka Bude Bayan Hutu