Gwamnatin Gombe ta amince ta fara biyan mafi karancin albashi

Gwamnan jihar ya jaddada cewa jin daɗin ma’aikata na daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa.

Gwamnatin Gombe ta amince ta fara biyan mafi karancin albashi

Gwamnatin Jihar Gombe ta sake jaddada aniyarta na inganta jin daɗin ma’aikata, inda ta amince da fara biyan cikakken sabon mafi ƙarancin albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi, sashen ilimi da lafiya a faɗin jihar.

Wannan mataki ya biyo bayan kammala biyan ragowar kashi 43 cikin 100 na sabon tsarin albashin, lamarin da ya tabbatar da cewa yanzu an kai matakin aiwatar da shi zuwa kashi 100 cikin 100.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar, Farfesa Mu’azu Shehu, ya fitar, inda ya bayyana cewa za a fara aiwatar da sabon tsarin albashin daga watan Mayun 2026.

Ya ce wannan ci gaba ya samo asali ne daga bunkasar yanayin kuɗi a matakin ƙananan hukumomi, wanda ya bai wa hukumomi damar biyan albashi cikin sauƙi ba tare da jinkiri ba.

A cewarsa, sabon albashin zai ƙara ƙaimi da kwazon ma’aikata, ya inganta gudanar da ayyukan gwamnati a matakin ƙasa.

Jihar Gombe na ci gaba da kasancewa cikin jihohin da suka fara aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi tun bayan amincewa da shi a shekarar 2024.

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya sha jaddada cewa jin daɗin ma’aikata na daga cikin manyan manufofin gwamnatinsa, yana mai cewa hakan na da matuƙar tasiri wajen bunƙasa ci gaban jihar.