Gwamnatin Gombe ta biya diyan fiye da miliyan 875

Jihar Gombe ta biya ta biya diyyan Naira miliyan dari 875 da dubu dari 214 na ayyukan kwangiloli da ta gudanar a jihar. Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Alhassan Ibrahim Kwami ya ce diyyar da aka biya ta hada da na mallakar fili da kuma biyan kudaden wasu kadarori da aka yi a lokacin da ake […]

Gwamnatin Gombe ta biya diyan fiye da miliyan 875

Daga dama Kwamishinan Yada Labarai, Alhassan Ibrahim Kwami da Kwamishinan Ruwa Mijinyawa Yahaya a lokacin zantawar,

Jihar Gombe ta biya ta biya diyyan Naira miliyan dari 875 da dubu dari 214 na ayyukan kwangiloli da ta gudanar a jihar.

Kwamishinan Yada Labaran Jihar, Alhassan Ibrahim Kwami ya ce diyyar da aka biya ta hada da na mallakar fili da kuma biyan kudaden wasu kadarori da aka yi a lokacin da ake gina hanyoyi a Jihar.

Ya bayyana hakan ranar Laraba bayan kammala zaman Majalisar Zartarwar Jihar na karshen shekarar 2020 wanda kuma shi ne zama na 10 da majalisar ta yi a shekarar.

Kwamishinan ya ce hanyar da aka gina daga unguwar Bamusa zuwa Yelanguruza da ta Kurba zuwa garin Titi an biya diya sama da Naira miliyan 79.

Sai diyar da aka biya kamfanin samar da hasken wutar lantarki na JED na kadarorinsu Naira miliyan 143.

Ya kara da cewa akwai kashi na biyu na gine-gine na kamfanin na JED da aka biya da ya haura naira miliyan 157, sai babbar masana’anta ta zamani da ake ginawa a garin Dadin-kowa an biya Naira miliyan 80.

Ya ce a kokarin Gwamnatin Jihar na samar da tsaro ta sayi falayen gonaki kusa da filin jirgin sama, don samar wa da sojin sama sansani na musamman wanda zai kula da shiyyar Arewa maso Gabas inda aka biya Naira miliyan 34, da dubu 805 da 677.

Gwamnatin ta kuma sake mallakar fili mai girman kadada 207 a rukunin filayen da ake kira GDP 34.

Ta sayi wasu gidaje da ke hade da Gidan Gwamnati kan Naira miliyan 23 don fadada girman gidan gwamnatin ya kuma zama cikin tsaro.

Daga nan ya ce hanyoyin da aka yi a unguwar Jekadafari an biya mata diyan Naira miliyan 35, hanyar da ta tashi daga unguwar Gandu ta bi Masallacin Idi, zuwa Kasuwar Doya kuma an biya musu diya sama da miliyan 71 da 450 kuma yanzu gwamnati ba a bin ta bashi.