Gwamnatin Gombe ta fara mayar wa mutum 236 filayensu

A kwanakin baya ne aka samu rashin jituwa tsakanin gwamnatin Jihar Gombe da mutanen da suka mallaki filayen bayan Asibitin Koyarwa na Tarayya ba bisa ka’ida ba.An kwace filayen ne a watan Agustan bara lokacin da aka rika kai ruwa rana a tsakanin masu filayen da gwamnati kan karbe musu filayen.kwace filayen ya biyo bayan […]

Gwamnatin Gombe ta fara mayar wa mutum 236 filayensu
Gwamnatin Gombe ta fara mayar wa mutum 236 filayensu

A kwanakin baya ne aka samu rashin jituwa tsakanin gwamnatin Jihar Gombe da mutanen da suka mallaki filayen bayan Asibitin Koyarwa na Tarayya ba bisa ka’ida ba.
An kwace filayen ne a watan Agustan bara lokacin da aka rika kai ruwa rana a tsakanin masu filayen da gwamnati kan karbe musu filayen.
kwace filayen ya biyo bayan nada wani kwamiti ne da gwamnatin Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ta yi, da Alhaji Shehu Abubakar Durbi.
A ranar Talatar da ta gabata ne kwamitin na Alhaji Shehu Durbi, ya fa mayar wa mutum tara daga cikin mutum 236 filayensu kuma aka ba su wa’adin wata biyu idan ba za su gina ba su kewaye don gudun kada a sake samun wata matsala.
Alhaji Shehu Durbi, ya ce tun farko an karbe filayen ne saboda gwamnatin da ta gabata ne ta sayar musu ba bisa ka’ida ba wanda hakan ya jawo canja tsarin taswirar jihar. Ya ce wadanda aka kwace filayensu gwamnati ta tabbatar da cewa za a ba su wasu filaye na daban.
Wasu daga cikin wadanda aka mayar wa filayensu Rabaran Daniel Timothy Burak, Shugaban riko na karamar Hukumar Shongom da tsohuwar Kwamishinar Mata, Asma’u Muhammad Iganus, sun nuna farin cikinsu kan yadda aka mayar musu da filayensu tare da gode wa gwamnati.