Gwamnatin Gombe ta horar da makiyaya kan sabbin hanyoyin kiwo

Gwamnatin ta ce ta shirya horon ne duba da yadda buƙatar awaki ke ƙaruwa a duniya.

Gwamnatin Gombe ta horar da makiyaya kan sabbin hanyoyin kiwo

Gwamnatin Jihar Gombe ta horar da makiyaya 684, ciki har da nakasassu, mata, matasa, da tsofaffin ma’aikata, kan sabbin dabarun kiwon awaki da kasuwancinsu.

Wannan horo ya gudana ne ƙarƙashin shirin Livestock Productivity and Resilience Support (L-PRES).

Kwamishinan Aikin Gona, Kiwo, da Hada-hadar Ƙungiyoyi na Jihar Gombe, Dokta Barnabas Malle ne, ya jagoranci ƙaddamar da horon a Gombe.

Yayin da yake jawabi, ya jaddada ƙudirin gwamnatin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, na inganta kiwon dabbobi da tallafa wa al’umma.

Ya ce: “Shirin ya dace da manufofin gwamnati na bai wa kowa damar cin gajiyar shirye-shiryen da ake gudanarwa.”

Shugaban shirin L-PRES na Gombe, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana cewa horon zai taimaka wa makiyaya wajen ƙara ƙwarewa da haɓaka kiwon awaki.

Ya ce: “Mun mayar da hankali kan makiyaya saboda muhimmiyar rawar da suke takawa wajen samar da awaki a tsakanin al’ummarmu.

“Manufarmu ita ce ƙara musu ƙwarin gwiwa da ƙwarewa don su inganta rayuwarsu.”

Farfesa Abubakar, ya ƙara da cewa buƙatar naman awaki a duniya na ƙaruwa, don haka Gombe na da shirin kafa cibiyar kiwon awaki ta zamani da kuma babbar kasuwa ta yanka dabbobi a Najeriya.

A yayin horon, an koyar da mahalarta yadda ake:

  • Zabar nau’in awaki masu inganci
  • Ciyarwa mai kyau
  • Rigakafin cututtuka
  • Inganta muhalli don kiwo

Dabarun kasuwanci da sarrafa kayayyakin da ake samu daga awaki

Shugaban Ƙungiyar Masu Nakasassu ta Jihar Gombe, Ja’o Sarkin Aiki, ya yaba wa gwamnatin bisa wannan horo

“Wannan horo zai taimaka mana wajen bunƙasa kiwonmu da kuma dogaro da kanmu don samun ingantacciyar rayuwa.”

An tara Naira 16 a taron ƙaddamar da littafin IBB

Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida

NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa

Ɗaliba ta rasu yayin da gini ya rufta a GGTC Potiskum