Gwamnatin Gombe ta nada sabon Sarkin Funakaye
Gabanin nadin nasa, sabon sarkin ya kasance mai rike da sarautar Dan Majen Funakaye.
Gwamnatin Jihar Gombe ta amince da nadin Alhaji Mu’azu Muhammad Kwairanga, Dan Majen Funakaye a matsayin sabon Sarkin Funakaye.
Sanarwar nadin sabon sarkin na kunshe ne a wata takarda dauke da sa hannun Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na Jihar, Ibrahim Dasuki Jalo Waziri, ranar Laraba.
A cewar takaradar, nadin ya biyo bayan dokar da ta sahale wa Gwamnan damar nadawa da sauke sarki bisa amincewar masu zabar sa da kuma shawarar kwararru.
Da yake mika wa sabon sarkin takardar nadin a Fadar Sarkin da ke garin Bajoga na Karamar Hukumar Funakaye, Kwamishinan ya hori sabon sarkin da ya rungumi kowa a matsayinsa na uban kasa.
Daga nan sai ya shaida wa sabon sarkin cewa lokacin wankan sarautar tare da ba shi sandar girma zai biyo baya nan gaba kadan.
Shi dai sabon sarkin, kani ne ga marigayi Sarki Muhammad Kwairanga Abubakar, da ya mutu mako biyu da suka gabata.
Gabanin nadin nasa, sabon Sarkin ya kasance mai rike da sarautar Dan Majen Funakaye.