Gwamnatin Gombe ta rushe gidajen Gala 5
An rushe gidajen ne saboda ba sa kan ka’ida
Kwamitin kar-ta-kwana da gwamnatin Jihar Gombe ta kafa kan rufe gidajen Gala ya kama mutum 100 sannan ya rushe gidajen Gala 5.
An rushe gidajen da kuma yin kamen me a yankunan unguwar Tumfure da BCGA da ke babban birnin Jihar.
Gidan Gala, dai waje ne da galibi matasa mata da maza ke haduwa ana rawa dan nishadantar da ’yan kallo akasari da daddare.
Sai dai mutane da dama na ganin gidan Gala a matsayin wajen lalata tarbiyyar yaran da sanya ’yan mata su shiga karuwanci.
An dai gudanar da aikin ne da hadin gwaiwar rundunar tsaro ta Sibil Difens (NSCDC).
A cewar Shugaban kwamitin Guruf Kyaftin Bitrus Bilal, rushe gidajen Galar ya biyo bayan umurnin gwamnati ne a daidai lokacin da ta haramta gudanar da ayyukan gidajen.
Ya kara da cewa masu gidajen da aka rushe din ba su da takardar izini ta mallakar filaye daga Hukumar Tsara Birane ta Jihar (GOSUPDA).
“Mun samu duka gidajen ba su da lasisi daga hukumar da ta dace. Wani abin takaici ma shi ne aikace-aikacensu ya saba tsarin al’adarmu,” in ji Bitrus.
Shugaban kwamitin ya kuma ce daga yanzu babu wani gidan Gala da za a sake budewa a ciki da wajen jihar kuma sun daura damarar yaki da masu irin wadannan baragurbin sana’o’i.
Da yake magana kan kama mutane 100, Kwamandan hukumar NSCDC a Jihar, Muhammad Bello Mu’azu, cewa ya yi wadanda aka kama din sun karya dokar da gwamnati ta gindaya ta kulle gidajen Galar.
Ya kuma ce za su tura wadanda aka kama din zuwa kotu domin su girbi abin da suka shuka da zarar sun kammala bincike a kan su.