Gwamnatin Gombe ta sake horar da matasa 1,554 kan aikin da’a
Gwamnatin Jihar Gombe ta sake daukar matasa 1,554 don koya musu aikin da’a na Marshal a garin Malam Sidi.Da yake kaddamar da fara samun horon karo na biyu, Gwamna Ibrahim dankwambo wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Abubakar Sule bage ya wakilta ya ce an dauki matasa karo na farkon ne a watan Mayun shekarar 2012.Ya […]

Gwamnatin Jihar Gombe ta sake daukar matasa 1,554 don koya musu aikin da’a na Marshal a garin Malam Sidi.
Da yake kaddamar da fara samun horon karo na biyu, Gwamna Ibrahim dankwambo wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Abubakar Sule bage ya wakilta ya ce an dauki matasa karo na farkon ne a watan Mayun shekarar 2012.
Ya ce ganin yadda a wannan karon matasa suka ba da hadin kai wajen halartar wurin ba su horon, ya sa Gwamnan ya yaba musu domin ya nuna cewa suna kaunar wannan shiri da aka shirya dominsu.
Gwamna dankwambo, ya ce duk da cewa an kirkiro da shirin ne domin matasa ’yan Kalare sai ga shi mafi yawa daga cikin matasan ba ’yan Kalare ba ne wadanda shirin ya burge su suka kai kansu.
Sai ya yi kira ga malamam addini da sarakuna su ba da tasu gudunmawar wajen ganin an ci gaba da gyara tarbiyyar matasa a jihar.
Kwamishinan Matasa na Jihar Alhaji Mijinyawa Sani Labaran, gode wa Gwamna dankwambo ya yi bisa yadda ya damu da gyaran tarbiyyar matasa da samar musu da aiki don su dogaro da kansu.
Kwamishinan ya kuma gode wa shugabannin kananan hukumomin Kwami da Funakaye da Mai Martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Sulaiman kan yadda suka tallafa wa matasan da shanu don a yanka musu a lokacin da suke samun horo.
Mista Ado Solomon, Daraktan Hukumar Wayar da Kan Jama’a kuma Daraktan Sansanin cewa ya yi matasan fararen hula ne amma yanzu sun sami horo daga soja wanda hakan ya canja su kwata-kwata suka zama kamar sojoji.
Ya ce a karo na farko an samu mace daya amma yanzu akwai mata har takwas da suka ce su ma sai an yi da su.
Matasan za su samu horo na tsawon mako uku kuma sun kasu kashi uku ne da suka hada da jami’an tsabtace gari da dogarawan hanya da kuma jami’an kula da tsaron unguwanni.